Shugaban kasa Tinubu ya ta ya Trump murnan lashe zaɓe.
Shugaba Bola Tinubu ya mika sakon taya murna ga Shugaba Donald Trump kan sake zabensa a matsayin shugaban kasar Amurka na 47.
Cikin wata sanarwa da aka fitar yau mai dauke da sa hanun mai ba wa shugaban kasa shawara na musamman Bayo Onanuga ya ce shugaba Tinubu na fatan karfafa alakar Najeriya da Amurka a cikin harkokin kasuwanci da na diplomasiyya.
Shugaba Tinubu ya ce, “Tare, za mu iya inganta tattalin arziki, da inganta zaman lafiya, da magance kalubalen duniya da suka shafi ‘yan kasarmu.”
A cewar shugaba Tinubu nasarar da Trump ya samu na nuni da irin amana da amincewar da jama’ar Amurka suka yi a kan shugabancinsa. Ya na mai ta ya su murna bisa jajircewarsu na tabbatar da dimokradiyya.
Shugaba Tinubu ya yi imanin cewa, idan aka yi la’akari da kwarewar Shugaba Trump a matsayin shugaban Amurka na 45 daga 2017 zuwa 2021, komawar sa fadar White House a matsayin shugaban kasa na 47 zai haifar fa’ida, tare da inganta tattalin arziki da ci gaba tsakanin Afirka. da Amurka.