Shugaba Tinubu zai bar Abuja zuwa kasar Saudiyya

Shugaba Tinubu ya tafi kasar Saudiyya domin halartar taron hadin gwiwa na kasashen Larabawa

Spread the love

Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai bar Abuja ranar Lahadi zuwa birnin Riyadh na kasar Saudiyya domin halartar taron hadin gwiwa tsakanin kasashen Larabawa da Musulunci.

Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan yada labarai Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranar Asabar, ya ce taron zai mayar da hankali ne kan halin da ake ciki a yankin gabas ta tsakiya.

Ana sa ran fara taron a ranar Litinin 11 ga Nuwamba, 2024.
A cewar Onanuga, ana gudanar da taron ne bisa gayyatar Sarki Salman da Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman, kuma ya biyo bayan taron da aka yi a shekarar da ta gabata a birnin na Saudiyya.

Ya ce, “A yayin taron, ana sa ran shugaba Tinubu zai yi jawabi kan rikicin Isra’ila da Falasdinu, inda ya jaddada kiran da Najeriya kan a tsagaita bude wuta cikin gaggawa da warware rikicin cikin lumana.


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button