Shettima ya amince da Sanusi a matsayin Sarkin Kano na 16

Wani martani ya biyo bayan amincewa da Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano na 16 da mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya yi

Spread the love

Daily trust ta ruwaito cewa Mataimakin Shugaban kasa a shafinsa na Facebook da X ya yi wa Sanusi lakabi da Sarki na 16, lamarin da ya sa masu amfani da shafukan sada zumunta suka mayar da martani da suka dauka a matsayin amincewar Sanusi na sarautar Kano.

 

Yayin da rikicin Masarautar Kano ke ci gaba da kasancewa a gaban kotu, jihar ta shaidi samun sarakuna biyu wato Sanusi da na 15, Aminu Ado Bayero.

 

Rubutun da ya wallafa na cewa; “A ranar Asabar, na halarci daurin auren Fatiha diyar tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabi’u Kwankwaso.

 

Kwankwaso ya aurar da diyarsa, Dr. Aishatu Kwankwaso da Fahad, dan hamshakin dan kasuwan nan mazaunin Katsina, Alhaji Dahiru Mangal.

 

“Babban limamin Kano Farfesa Sani Zahraddeen ne ya gudanar da daurin auren a fadar mai martaba Sarkin Kano na 16, Alhaji Muhammadu Sanusi II.

 

Sai dai bayan wasu martani da masu amfani da shafukan sada zumunta suka yi, daga baya aka gyara sakin layi na uku a cikin sakon tare da cire sunan sarki.

 

Inda rubutun ya koma kamar haka; “Babban limamin Kano, Farfesa Sani Zahraddeen ne ya gudanar da daurin auren a fadar Sarkin Kano.”

 

Da yake mayar da martani, wani mai amfani da kafafen sada zumunta, Alhassan Ali Lawan ya ce, “Mun yi farin ciki da karrama wannan gayyata mai girma! Muna kuma farin cikin amincewa da Sarkinmu a matsayin Sarkin Kano na 16. Dan takarar shugaban kasa (Rabiu Musa Kwankwaso PhD) yana muku fatan alheri da dawowa gida! Godiya sake!!!”

 

Wani mai suna Najeeb Sule Alfindi ya ce, “Mafi kyawun sakin layi da ya burge ni shi ne sakin layi na 3, inda ka ce wanda ya faru a fadar Sarkin Kano, sannan ka ambaci wanene Sarki Muhammad Sunusi na biyu. Na gode Sir.”

 

Musa Kabir ya rubuta, “Masha Allah! Mai girma gwamna a madadin mutanen jihar Kano mun yaba da zuwan ku. Na san za ku iya hada shiyoyin goepolitical zones guda shida a kasar nan. Na biyu ina matukar jin dadin maganarka ta biyu wacce ta kira Sarkin Kano na 16. Malam Sunusi Lamido Sunusi shine zabinmu kuma ina yi maka addu’a wata rana ka zama direban wannan al’umma.”


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button