Sarkin Musulmi ya nemi gwamnati ta hukunta masu daukar nauyin ta’addanci 2024
Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar, ya bukaci gwamnati ta fallasa tare da hukunta masu daukar nauyin ayykan ta’addanci
Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar, ya bukaci gwamnati ta fallasa tare da hukunta masu daukar nauyin ayykan ta’addanci
Majalisar Addinai ta Kasa (NIREC) ta bukaci gwamnatin tarayya da na jihohi su fallasa tare da hukunta masu daukar nauyin ayykan ta’addanci.
Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III tare Shugaban Kungiyar Kiristoci ta Nijeriya (CAN), Daniel Okoh ne suka yi kiran a wurin taron da suka gudanar a Abuja, kamar yadda jaridar trust radio ta rawaito.
Shugabannin addinan sun koka bisa mummunar illar da ayyukan ’yan bindiga da dangoginsu ke yi wa al’ummomi, gami da raba jama’a da muhallansu da lalata rayuwarsu da kuma mayar da su ’yan gudun hijira a cikin kasarsu.
Sarkin Musulmi ya bukaci ’yan Nijeriya su koma ga Allah su nemi rahamarSa da dawowar zaman lafiya da ci-gaban kasar.
Sarkin Musulmi ya kuma gargadi ’yan siyasa da su ji tsoron Allah su guji tara dukiya ta hanyar haram da kuma mara amfani.
A nasa bangare, Archbishop Okoh, ya jaddada muhimmancin shugabanni su alkinta albarkatun da Allah Ya huwace wa Nijeriya domin amfanin jama’a, maimakon su mayar da su tushen rikice-rikice da kuma rashin tsaro.
Shugaban addinin ya kuma yi kira da a karfafa bangaren shari’ar Nijeriya domin yin adalci da kuma hukunta masu yin zagon kasa ga ci-gaban kasa da kuma sha’anin tsaro.
Sakataren NIREC, Rabaran Cornelius Omonokhua, ya koka kan yadda ake wasu tsiraru ke cin moriyar ma’adinan Nijeriya ta hanyoyin da ke cutar da ’yan kasar a yankunan Kudu da Arewa.
Sarkin Musulmi ya bukaci ‘yan Najeriya da su ke yi wa shugabanni addu’a
Mai alfarma Sarkin Musulmi, Sa’ad Mohammad Abubakar II, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su guji sukar shugabanninsu, inda ya bukace su da su dogara ga Allah.
Da yake jawabi a wajen wani taron shiyya kan tashe-tashen hankula da suka haifar da sauyin yanayi a Arewacin Najeriya, wanda ofishin kula da harkokin addinai da na kasa da kasa reshen jihar Kaduna ya shirya, Sarkin Musulmi ya jaddada muhimmancin addu’a ga al’ummar kasa da kuma shugabanninta.
Ya tunatar da masu shugabanci cewa suke aiki saboda Allah Shi kadai domin samun sakayya a ranar kiyama, yana mai jaddada bukatar shugabanni su yi aiki da alhaki da tsoron Allah.
Da yake karin haske kan tasirin malaman addini, Sarkin Musulmi ya shawarce su da su guji yaudarar mabiyan su domin amfanin kansu. “Allah ne kaɗai ke da ikon ceton kowane ɗan adam,” in ji shi, Ya bukaci ‘yan Najeriya da su koma ga ibada da addu’a, musamman a lokutan tsanani. Inda ya shawarci al’umma da Kada su bi waɗanda za su iya batar da su, kasarmu tana fuskantar kalubale da dama, kuma dole ne mu koma ga Allah cikin addu’a,” inji shi.
Shugaban kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) ya halarci taron, inda ya nuna matsaya daya kan muhimmancin addu’o’in mabiya addinai ga al’umma.
Da yake jawabi a kan batutuwan da ke fuskantar arewacin Najeriya, da suka hada da sauyin yanayi, talauci, da rashin tsaro, Sarkin Musulmi ya bayyana tarihin tsayin daka da hadin kai a yankin a matsayin abinda zai gyara mana kasar nan yana yin gargadi game da yadda ake yada labaru dake rarraba kan al’umma wadda yace hadin kai ne mafitar k asar nan.
‘Yan sandan Najeriya sun kashe mutum 24 a zanga-zangar tsadar rayuwa ta watan Agusta – Amnesty
Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta ce binciken da ta yi kan yadda hukumomin Najeriya, suka murkushe zanga-zangar kin jinin gwamnati a watan Agusta, ya nuna cewa jami’an kasar sun kashe akalla masu zanga-zangar 24 tare da tsare wasu fiye da 1,200.
VOA tace, Rahoton mai shafuka 34 da Amnesty International ta fitar a ranar Alhamis, ya samo asali ne daga shaidun gani da ido da hirarraki da ma’aikatan lafiya da iyalai da abokan wadanda abin ya shafa.
Amnesty ta ce ‘yan sandan Najeriya sun yi amfani da karfin tuwo kan masu zanga-zangar da suka taru domin nuna adawa da tsadar rayuwa.
Ta ce ‘yan sanda sun kashe akalla mutane 24, ciki har da yara biyu. An samu asarar rayuka a fadin jihohin Borno da Kaduna da Kano da Katsina da Jigawa da kuma Neja.
A cewar rahoton, ‘yan sanda sun yi ta harbe-harbe kai tsaye a kusa da kan wadanda lamarin ya rutsa da su, yayin da wasu da abin ya shafa suka shaki hayaki mai sa hawaye.
Isa Sanusi, darektan kungiyar Amnesty a Najeriya, ya yi imanin cewa adadin wadanda suka mutu na iya karuwa sosai.
“Ko a yau da muke kaddamar da wannan rahoto a Kano, iyalai da dama sun fito suna shaida mana cewa ‘ya’yansu sun bace, wasu da dama kuma ana kyautata zaton an kashe su ko kuma ana tsare da su a asirce, don haka batun gaba daya ya fi yadda ake tsare da su. Wannan kawai ya nuna cewa hukumomin Najeriya ba su shirya amincewa da cewa jama’a na da ‘yancin yin zanga-zangar lumana ba.”
Zanga-zangar da aka yi a watan Agusta, wadda masu shirya ta suka kira “Ranaku Goma na Fushi”, ta kasance mayar da martani ne ga tsadar rayuwa da mutane da dama suka yi imani da cewa sauye-sauyen da Shugaba Bola Tinubu ya yi ne ya haifar da su, ciki har da cire tallafin man fetur.
Hukumomin ‘yan sandan Najeriya ba su mayar da martani kan zargin Amnesty ba, amma a baya sun musanta yin amfani da harsashi mai rai wajen dakile zanga-zangar.
Kakakin ‘yan sandan kasar bai amsa kiran da Muryar Amurka ta yi masa ba.
A cikin watan Oktobar 2020, zaluncin ‘yan sanda ya haifar da zanga-zangar adawa da Rundunar ‘yan sandan SARS.
Zanga-zangar dai ta kawo karshe ne sakamakon harbi da bindiga da aka yi a kofar karbar harajin Lekki da ke Legas.
Najeriya dai ta dade tana fama da ta’asar ‘yan sanda, duk kuwa da alkawuran da aka sha yi mata na cewa za ta kara kaimi.