Sarkin Musulmi ya bukaci ‘yan Najeriya da su ke yi wa shugabanni addu’a
Mai alfarma Sarkin Musulmi, Sa’ad Mohammad Abubakar II, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su guji sukar shugabanninsu, inda ya bukace su da su dogara ga Allah.
Da yake jawabi a wajen wani taron shiyya kan tashe-tashen hankula da suka haifar da sauyin yanayi a Arewacin Najeriya, wanda ofishin kula da harkokin addinai da na kasa da kasa reshen jihar Kaduna ya shirya, Sarkin Musulmi ya jaddada muhimmancin addu’a ga al’ummar kasa da kuma shugabanninta.
Ya tunatar da masu shugabanci cewa suke aiki saboda Allah Shi kadai domin samun sakayya a ranar kiyama, yana mai jaddada bukatar shugabanni su yi aiki da alhaki da tsoron Allah.
Da yake karin haske kan tasirin malaman addini, Sarkin Musulmi ya shawarce su da su guji yaudarar mabiyan su domin amfanin kansu. “Allah ne kaɗai ke da ikon ceton kowane ɗan adam,” in ji shi, Ya bukaci ‘yan Najeriya da su koma ga ibada da addu’a, musamman a lokutan tsanani. Inda ya shawarci al’umma da Kada su bi waɗanda za su iya batar da su, kasarmu tana fuskantar kalubale da dama, kuma dole ne mu koma ga Allah cikin addu’a,” inji shi.
Shugaban kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) ya halarci taron, inda ya nuna matsaya daya kan muhimmancin addu’o’in mabiya addinai ga al’umma.
Da yake jawabi a kan batutuwan da ke fuskantar arewacin Najeriya, da suka hada da sauyin yanayi, talauci, da rashin tsaro, Sarkin Musulmi ya bayyana tarihin tsayin daka da hadin kai a yankin a matsayin abinda zai gyara mana kasar nan yana yin gargadi game da yadda ake yada labaru dake rarraba kan al’umma wadda yace hadin kai ne mafitar k asar nan.