Sarkin Musulmi ya baiwa Pantami babbar Sarauta
Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya ba Farfesa Isa Ali Pantami sarautar Majidadin Daular Usmaniya.
A ranar Asabar din da ta gabata ne Sarkin Musulmi ya halarci taron shekara-shekara na Shaihu Usman Ibn Fodiyo karo na 11, inda Pantami ya gabatar da jawabi mai taken “Hadin kai a matsayin Maganganun Rashin Tsaro da Talauci: Darussan Jagororin Jlhadin Sakkwato”.
Bayan kammala laccar, Majalisar Sarkin Musulmi karkashin jagorancin Mai Martaba Abubakar, ta karrama tsohon Ministan Sadarwa da lambar yabo bisa irin gudunmawar da ya bayar a matsayinsa na jagoran addini da siyasa.
Sarkin da ake girmamawa ya bayyana irin rawar da Pantami ke yi a shirye-shiryen da suka yi dai-dai da hangen nesa na Sultanate na ci gaba da jin dadin al’umma.
“Farfesa Pantami ya nuna jajircewarsa wajen inganta rayuwar ‘yan Najeriya. Babban gudunmawar da ya bayar a fannin ilimi, hidimar jama’a, da ci gaban al’umma abin yabawa ne,” in ji Sultan Abubakar.
“Kokarin da ya yi na bayar da tallafin karatu ga daliban da ba su da galihu da kuma samar da guraben ayyukan yi ga kwararrun matasa ya yi tasiri sosai ga iyalai da dama, yana samar da bege da ci gaba a cikin al’ummomi daban-daban.”
Majalisar Sarkin Musulmin ta bayyana fatan cewa wannan karramawar za ta zaburar da sauran jama’a wajen gudanar da irin wannan hidimar, wanda ke nuni da akidar jin-kai da jagoranci da masarautar ta ke neman a tabbatar da ita.
Sakataren gwamnatin jihar Sokoto, Bello Sifawa, wanda ya wakilci gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya mika godiyarsa ga majalisar Sarkin Musulmi bisa karramawar da aka yi wa Pantami.
Da yake mayar da martani, Pantami ya godewa Alhaji Abubakar tare da alkawarin ci gaba da gudanar da ayyukansa na ilimi da aikin gwamnati. Tsohon Ministan ya bukaci daukacin ‘yan Najeriya da su hada kai wajen samar da kyakkyawar makoma ga al’ummar kasar.