Sanata Kawu ya bukaci gwamna Abba na Kano da ya tabbatar da adalci ga dukkan ‘yan kasa
Sanata Kawu ya bukaci gwamna Sanata Abdulrahman Suleman Kawu, mai wakiltar Kano ta Kudu, ya yi kira ga Gwamna Abba Yusuff da ya yi wa ‘yan Kano adalci, ba tare da la’akari da alakar siyasarsu ba.
A wata zantawa da manema labarai a karshen mako, Kawu ya jaddada mahimmancin amince wa da al’umma daban-daban na kusan mutane miliyan 20, inda ya bukaci gwamnan da kada ya fifita ‘yan kungiyar Kwankwasiyya fiye da sauran.
Yayin da yake fahimtar tasirin tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Rabi’u Kwankwaso, Kawu ya yi gargadi kan cin amanar jama’ar da suka goyi bayan zaben Yusuf.
Ya jaddada alhakin da ke wuyan gwamnan na kare hakkin dukkan ‘yan kasa, ciki har da na jam’iyyun adawa, ya kuma bayyana bukatar yin sulhu na gaskiya a fagen siyasa. Kawu ya ce duk wani nau’i na zalunci zai iya haifar da gazawa a ayyukan mulkin Yusuf.