Sabuwar kungiyar ta’addanci, ta Lakurawa, sun kashe utane 15, sun sace shanu 100 a birnin Kebbi
Rahotanni sun ce sabuwar kungiyar ‘yan bindiga da aka fi sani da Lakurawa ta kashe mutane 15 tare da yin awon gaba da shanu sama da 100 a garin Mera da ke karamar hukumar Augie a jihar Kebbi.
Wani mutumin garin, Alhaji Bashir Isah Mera (Yariman Mera), ne ya tabbatar wa Aminiya , ya ce ‘yan kungiyar sun mamaye garin ne a daidai lokacin da jama’a ke shirin Sallar Juma’a tare da kwashe shanu sama da 100.
Mera ya kara da cewa, ‘yan Lukarawa suna buya ne a dajin Sakkwato daga inda suke shirya kai hare-haren na su.
Duk ko karin jin ta bakin Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi, SP Nafiu Abubakar, yaci tura har zuwa lokacin hada wannan rahoto.