Sabon shugaban Sri Lanka ya gode wa jama’a saboda zaɓar jam’iyyarsa
Sabon shugaban Sri Lanka ya gode wa masu kaɗa ƙuri'a saboda yadda suka bai wa jam'iyyarsa mai sassaucin ra'ayi damar jagorantar gwamnatin haɗaka a zaɓen cike gurbi na ƴan majalisa.
BBC Hausa ta ruwaito cewar Sakamakon zaɓen ya bayyana irin adawar da ƴan kasar suke yi da yanayin matsin tattalin arziki da gwamnatocin baya suka jefasu.
Gagarumar nasarar da ya samu za ta taimaka masa wajen farfaɗo da tattalin arziki da kawo sauyi a siyasa, alwashin da ya ɗauka lokacin yakin neman zabe.
Gwamnatin Haɗakar ta samu kusan kashi 62 na kuri’u har a yankin Jaffna da ke kudancin Sri Lanka a karon farko tun bayan samun yancin kai daga Birtaniya.
Zaɓaɓɓen shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da Robbert Kennedy JR a matsayin sakataren lafiya na ƙasar.
Mukamin da ya bai wa Robert Kennedy Junior wani abu ne da zai janyo rarrabuwar kawuna tsakanin ‘yan majalisa musamman na adawa.
A jawabin da ya yi daga wurin shakatawa na Mar-a-lago, Mr Trump ya yaba wa Mr Kennedy, inda ya ce babu wanda zai iya aikin inganta fannin lafiya a Amurka kamar shi.
Kennedy mutum ne mai janyo cece-kuce kan allurar riga-kafi, musamman ra’ayinsa na nuna shakku kan riga-kafi lokacin annobar Korona.