Rundunar ‘yan sanda ta tsare jami’an ta 4 bisa karbar cin hanci miliyan 10 a Bayelsa
Hedikwatar ‘yan sanda da ke Abuja ta bayar da umarnin tsare wasu ‘yan sanda hudu bisa zarginsu da karbar Naira miliyan 10 daga wasu matasa a jihar Bayelsa.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar, ACP Muyiwa Adejobi, ya bayyana jami’an da ake zargi dasuka hada da Emmanuel Ubong, mataimakin sufeton ‘yan sanda (ASP); Nse Okon, Adiewere Collins, da Kuromare Marine — duk sufetocin ‘yan sanda.
Adejobi ya ce an kwato kudaden ne ta hanyar kokarin Adebola Hamzat, sabon mataimakin sufeto-janar na rundunar ‘yan sanda (AIG) da ke jagorantar shiyya ta 16 na rundunar, inda ya ce za a gurfanar da jami’an gaban kotu.
Ya ci gaba da cewa IGP Egbetokun ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan zargin cin hanci da rashawa da ake yi wa jami’an.
Ya ce, Sufeto-Janar na ‘yan sanda, IGP Kayode Adeolu Egbetokun, ya yi Allah-wadai da zargin karbar cin hanci da wasu jami’an rundunar sukayi, musamman batun da ya shafi jami’an hedikwatar shiyya ta 16, Yenegoa.