Rikicin Siyasar Kumbotso: Hardwoker zai garzaya kotu

Rikicin Siyasar Kumbotso: Hardwoker zai garzaya kotu don ƙalubalantar rantsar da Basaf a matsayin Ciyaman

Spread the love

Rikicin Siyasar Kumbotso: Hardwoker zai garzaya kotu don ƙalubalantar rantsar da Basaf a matsayin Ciyaman

Dan takarar shugabancin ƙaramar hukumar Kumbotso a jam’iyyar NNPP, Ali Musa Danmaliki, wanda aka fi sani da Hardworker, ta bakin lauyoyin sa, ya ci alwashin zuwa kotu domin ƙalubalantar rantsar da Ghali Shitu, wanda aka fi sani da Basaf a matsayin Ciyaman.

Lauyoyin Hardwoker, a wani taron manema labarai a Kano, sun zargi gwamnatin Kano da sabawa umarnin kotu wajen rantsar da Basaf a matsayin shugaban karamar hukumar.

Idan za a iya tunawa dai a ranar Juma’a kwamishinan shari’a na jihar Kano ya rantsar da Basaf a matsayin shugaban karamar hukumar Kumbotso bisa jagorancin gwamna Abba Kabir Yusuf.

Tun da fari, NNPP ta tsayar da Hardwoker a matsayin ɗan takarar ciyaman na Kumbotso, amma daga bisani sai ta sauya shi da Basaf.

Daga nan ne sai Hardwoker ya garzaya kotu, inda a karshe ta samu nasara a kotun a ranar 25 ga watan Oktoba, ana i gobe zaɓe cewa shi ne halastaccen dan takarar amma jam’iyar NNPP ta ƙi bin umarnin kotu.

Da ya ke bayani ga manema labarai a Kano, Lauyan Hardwoker, Jazuli Mustapha ya ce Gwamnatin Kano bata yi biyayya ga umarnin kotun ba wanda ya ce umarnin ya hana rantsar da kowa.

Lauyan ya ce tun da farko wanda suke wakilta ya garzaya kotu bisa zargin rashin adalci da jam’iyyar tayi masa na sauya sunansa bayan ya siyi fom din takara.

Lauyan ya ce a ranar 25 ga watan Oktoba, kotu ta tabbatar da wanda suke wakilta a matsayin halastaccen dan takara.

“Bayan wannan hukunci jam’iyya ta daukaka kara, shi wanda jam’iyya ta sauya da shi wato Ghali Abdullahi Shitu, yazo da roko gaban kotu kan cewa kotu ta jinginar da hukuncin da tayi.

“Daga nan jam’iyya ta kawo roko kotu na dakatar da zartar da hukuncin farko da tayi har sai an dawo daga kotun daukaka kara, bayan sauraron wannan. roko , kotu tayi hukuncin ta kuma kowa yaji abinda ya faru a kotun”.

Barista Jazuli ya yi ikirarin cewa kotun ta ce kada a rantsar da kowa amma daga baya suka ga an rantsar da Ghali Abdullahi Shitu.

Lauyan wanda ya bayyana lamarin da cewa rashin da’a ne , ya ce zasu dauki matakan da suka dace na shari’a don ƙalubalantar rantsar da Basaf din.


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button