Rikicin Kwankwaso da Abba

Rikici na neman ɓarkewa tsakanin Kwankwaso da Abba bayan da gwamnan ya dena ɗaga wayar mai gidan nasa.

Spread the love

Rikicin da ke cikin jam’iyyar NNPP mai mulki a Kano na neman ƙazancewa, inda gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf ya fara ƙin daga wayar mai gidansa Rabi’u Musa Kwankwaso sannan ya ƙi halartar tarukan da jagoran NNPP din na kasa ya shirya.

Da alama dai wannan taken na “Abba tsaya da kafar ka” ya fara tasiri a gurin gwamnan bayan da wasu ke ta motsa yadda zai karɓe iko da jam’iyyar da kuma Kwankwasiyya daga hannun Kwankwaso.

Wasu majiyoyi sun shaidawa DAILY NIGERIAN cewa tuni Abba ya fara amsa kira bayan da “aka nusar da shi cewa Kwankwaso ne ke juya gwamnatin sa inda kusan kashi 90 na makaman da Abba ya yi daga ɓangaren Kwankwaso ne.”

Majiyoyi sun baiyana cewa Abba ba ya jin daɗin “ƙarfa-ƙarfa” da Kwankwaso ya ke yi masa inda ya ya fara nuna alamun boyewa masu kira da ya tsaya da kafar sa domin ci gaban sa na siyasa da ma jihar Kano baki ɗaya.

Tun lokacin da aka ga gwamnan a bikin murnar zagayowar haihuwar Kwankwaso, har yanzu basu sake haduwa ba.

Majiyoyi sun baiyana wa DAILY NIGERIAN cewa duk tarukan da Kwankwaso ya kira a Kano da Abuja Abban bai halarta ba.

Majiyoyin sun kara da cewa har Abuja Kwankwaso ya bi gwamnan amma Abba bai bari sun hadu ba, kuma har dan aike ya tura amma Abban ya ki ganuwa a wajen Kwankwaso.

Hakan na zuwa ne yayin da yan majalisar wakilai biyu, Ali Madaki mai wakiltar Dala da Alhassan Rurum mai wakiltar Rano da Kibiya su ka fice daga Kwankwasiyya a jiya Lahadi, wani lamari da ya kara fito da rikon da ke cikin jam’iyyar.

“Yanzu haka ana shirin hada kai da wasu ƴan APC da yan kungiyar Abba Tsaya da Kafar ka wajen samo umarnin kotu da zai kori dukka waɗannan ciyamomin da aka rantsar sai a hana CBN da ma’aikatar kudi ta hana su kudin wata-wata sai dai a baiwa tsagin da Mai Shari’a Simon Amobeda ya tabbatar ana i gobe zaɓe,” in ji majiyar.S

ai dai Daily Nigerian ta gaza jin ya bakin Kwankwaso, amma wani na jikin sa ya nuna rashin jin dadin halaiyar da Abba ke nunawa Kwankwason.

Shi ma mai magana da yaqin Abba, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya ki cewa uffan akan batun.


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button