Nahcon ta mayar wa alhazan Najeriya naira biliyan 5.3 saboda rashin kulawa a aikin hajji
Hukumar aikin hajji ta mayar da hukumomin alhazai na jihohin da ba su samu cikakkiyar kulawar hukumar ba lokacin aikin hajjin da ya gabata na 2023.
Hukumar alhazan Najeriya ta mayar da hukumomin alhazai na jihohin da ba su samu cikakkiyar kulawar hukumar ba lokacin aikin hajji wanda ya gabata na 2023.
BBC hausa tace, Cikin wani saƙo da Nahcon ɗin ta wallafa a shafinta na Facebook, ta ce kuɗin wanda ya kai naira biliyan 5.3, ta ce ta mayar wa hukumomin alhazai na jihohin da kamfanonin shirya tafiye-tafiyen da ba su samu kulawar da ta dace ba a lokacin aikin hajjin da ya gabata.
Wasu jihohin ƙasar da ma kamfanonin shirya tafiye-tafiye sun bayyana ƙorafe-ƙorafensu bayan kammala aikin hajin kan abin da suka kira rashin ingancin aiki da rashin kulawa daga hukumar alhazai ta ƙasar.
Inda wasu da dama suka zargi hukumar alhazan ƙasar da karkatar da wani ɓangare na kuɗaɗen tallafin aikin hajji da gwamnatin tarayya ta bayar, wani abu da wasu ke alaƙanta wa da korar tsohon shugaban hukumar alhazan ƙasar, Malam Jalal Ahmad Arabi.
An sake zaɓar Okonjo-Iweala shugabar WTO a wa’adi na biyu
Ƙungiyar Cinikayya ta Duniya, WTO ta sake zaɓar Dakta Ngozi Okonjo-Iweala a matsayin shugabanta a wa’adin mulki na biyu, inda za ta ci gaba da jagorantar ƙungiyar har zuwa 2029.
Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da harkokin cinikayyar duniya ke cikin wani mawuyacin yanayi.
A farkon makon nan zaɓaɓɓen shugaban Amurka, Donald Trump ya ce zai ƙaƙaba sabbin haraje-harajen cinikayya da ƙasashen Canada da Mexico da China idan ya kama aiki cikin watan Janairu.
A lokacin wa’adin mulkinsa na farko, Donald Trump ya yi yunƙurin hana Ms Okonjo-Iweala samun matsayin, inda ta samu nasarar ɗarewa muƙamin bayan Joe Biden ya zama shugaban Amurka.
Babban abin tambaya a yanzu shi ne irin tasirin da ƙungiyoyin kasuwanci irin WTO za su yi, a daidai lokacin da manyan ƙasashe mafiya ƙarfin tattalin arziki ke ƙara samun saɓanin kasuwanci.
Ga kuma batun yaƙin Ukraine da ya haifar da ƙarin takunkuman kasuwancin tsakanin wasu manyan ƙasashe.
‘Yan majalisa Birtaniya sun goyi bayan ƙudirin dokar taimaka wa marasa lafiya su mutu
Yan majalisar dokokin Birtaniya sun goyi bayan daftarin ƙudirin da zai halasta taimaka wa marasa lafiya da ke cikin tsanani su mutu.
Ƙudirin dokar zai bai wa mutanen da ke da sauran ƙasa da wata shida a rayuwa su yanke hukuncin ko suna so a kashe kansu.
Wannan tanadin dokar zai zamo mai matuƙar wuyar aiwatarwa saboda dole ne sai an samu likitoci biyu da za su tabbatar cewa mutum yana da sauran ƙasa da wata biyu a rayuwarsa ta duniya.
Ƴar majalisar da ta gabatar da ƙudirin, Kim Leadbeater ta ce burin nata, wata hanya ce ta bai wa mutane damar mutuwa cikin mutunci.
Maniyyata za su fara ajiye N8.4m kafin alkalami na aiki hajjin 2025 a Kaduna
Hukumar ta ce ta ɓullo da hanyar ne domin sauƙaƙa wa manoma yadda za su biyan kuɗin aikin hajjin 2025.
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kaduna, ta sanar da cewa, maniyyata za su iya fara biyan aƙalla Naira miliyan 8.4 a matsayin kuɗin aikin Hajjin 2025.
Hukumar ta kuma bayyana cewa an fara rijistar Hajjin 2025 a dukkanin ƙananan hukumomin 23 jihar.
Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Yunusa Mohammed Abdullahi ne, ya bayyana haka a wani shirin gidan rediyo a jihar.
Ya jaddada muhimmancin bin ƙa’idojin rijista a ƙananan hukumominsu.
Ya kuma bayyana cewa an samar da tsarin biyan kuɗin ne domin sauƙaƙa wa manoma.
Manoma za su biya aƙalla Naira miliyan 4.5 a matsayin ajiya, sannan su biya ragowar kuɗin bayan an girbe amfanin gona, amma cikin wa’adin da gwamnatin jihar ta ƙayyade.
Hukumar ta shawarci dukkanin masu niyyar zuwa aikin Hajjin su fara rijistarsu a kan lokaci kuma su bi ƙa’idojin da hukumar ta shimfiɗa.