Obasanjo yayiwa Aiyedatiwa fatan alkhairi gabannin zaben Ondo dake tafe

Spread the love

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya mika sakon fatan alheri ga gwamna Lucky Aiyedatiwa gabanin zaben gwamnan jihar Ondo da za a yi ranar Asabar.

Obasanjo ya bayyana haka ne a ranar Litinin a Akure, babban birnin jihar, a lokacin da ya ziyarci Aiyedatiwa a gidan gwamnati.

Tsohon shugaban kasar ya ce ba abu ne mai sauki ba daga wannan wuri zuwa wancan, yana neman kuri’u da goyon bayan jama’a.

Ya jinjinawa jajircewar Aiyedatiwa wajen isar wa jama’a da tsare-tsare da shirye-shiryensa, tare da yi wa gwamna fatan alheri a zaben.

Obasanjo ya fahimci kalubalen wannan lokacin, inda yace tuna yakin neman zabe na 1999. Na rufe dukkan jihohin shida na kudu maso yamma gaba daya a rana daya.

Ina tsammanin mun fara daga Akure, Jihar Ondo a nan, sai Ekiti muka isa Legas da misalin karfe 8 na dare. Wannan wani muhimmin bangare ne na tsarin kuma ina yi muku fatan alheri, in ji tsohon shugaban kasar.

Aiyedatiwa ya amince da irin gudunmawar da tsohon shugaban kasar ya bayar wajen ci gaban Najeriya, inda ya kara da cewa nasarorin da ya samu har yanzu ba za su gushe ba.

Ya ce duk da irin martabar sa da kuma matsayinsa na soja, Obasanjo ya kasance shugaba mai tawali’u da mutuntaka.


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button