Nijar ta dakatar da watsa shirye-shiryen BBC na wata uku a tashoshin FM 2024

Gwamnatin mulkin soji a Jamhuriyar Nijar ta dakatar da watsa shirye-shiryen rediyo na BBC a tashoshin FM a fadin kasar har na tsawon wata uku.

Spread the love

Gwamnatin mulkin soji a Jamhuriyar Nijar ta dakatar da watsa shirye-shiryen rediyo na BBC a tashoshin FM a fadin kasar har na tsawon wata uku.

Nijar ta dakatar da watsa shirye-shiryen BBC na wata uku a tashoshin FM
Nijar

Sanarwar da gwamnatin kasar ta fitar, ta zargi BBC da watsa labaran da ba haka suke ba, wadanda ke iya rage karsashin sojojin da ke yaki da masu ikirarin jihadi.

Ministan sadarwa a Nijar, Sidi Mohammed Raliou, a cikin wata sanarwa da ya fitar ya zargi gidan rediyon BBC da yaɗa labarai masu cike da kura-kurai waɗanda za su iya kawo tarnaƙi wajen samar da zaman lafiya a Nijar.

A cewarsa, a kan haka ne suka ɗauki matakin dakatar da watsa shirye-shiryen BBC na tsawon wata uku a tashoshin FM da ke faɗin ƙasar.

A cikin ƴan kwanakin nan BBC a harsunan Hausa da Faransanci da Ingilishi na bayar da rahotanni a kan lamuran da suka shafi tsaro, musamman irin gumurzun da ake yi tsakanin sojoji da kuma masu iƙirarin jihadi.

Wannan matakin na nufin a yanzu masu sauraron sashen Hausa na BBC da kuma sashen Faranshi na BBC sai dai su saurari shirye-shiryen tashoshin a mita mai gajeren zango ko kuma ta shafin intanet.

Tun a shekarar 1994, BBC ta ƙulla ƙawance da wasu gidajen rediyo masu zaman kansu da ke watsa shirye-shiryenta a zagon FM.

Wannan shi ne karo na farko da wata gwamnati a ƙasar ke dakatar da watsa shirye-shiryen BBC.

Ko a farkon watan Augustan 2023, ƴan kwanaki bayan juyin mulkin da sojojin suka yi sun dakatar da watsa shirye-shiryen gidan rediyon RFI da Talabijin na France 24 na ƙasar Faransa bisa zargin neman tayar da zaune tsaye.

A wani matakin na daban da gwamnatin mulkin sojan ta ɗauka a zaman majalisar ministocin da aka yi ranar Alhamis, ta ƙuduri aniyar maka gidan rediyon Faransa (RFI) kotu bisa zargin kafar da neman haddasa fitina tsakanin al’umma da “nufin haifar da kisan ƙare-dangi.”

Tun bayan komawa mulkin soji, hukumomin Nijar sun kama tare da tsare ‘yan jarida da ‘yan kungiyoyin fararen hula, wani abu da ake yi wa kallon salo ne na take ’yancin fadin albarkacin baki da kuma ‘yancin dan’adam.

Ko a wannan mako kungiyar kare hakkin bil’adama ta Human Rights Watch ta bukaci hukumomin na Nijar da su gaggauta sako wani dan kungiyar fararen hula, Moussa Tchangari, wanda aka kama a cikin wannan wata na Disamba bayan komawa gida daga wata tafiya da ya yi zuwa kasar ketare.

A ranar 26 ga watan Yulin 2023 ne sojoji suka tuntsurar da gwamnatin shugaban Nijar, Mohamed Bazoum bayan wani juyin mulki da suka gudanar, inda shugaban dakaru masu tsaron fadar shugaban ƙasar, Janar Abdourahamane Tchiani ya ayyana kansa a matsayin shugaban mulkin soji na ƙasar.

Daga baya Nijar da ƙasashe biyu masu maƙwaftaka da ita – Mali da Burkina Faso – sun haɗa kai tare da samar da ƙungiyar ƙasashen yankin Sahel (AES) tare da bayyana ficewar su daga ƙungiyar ƙasashen yammacin Afirka ta Ecowas/Cedeao.

Haka nan Jamhuriyar ta Nijar ta katse hulɗar dangantaka tsakaninta da uwar gijiyarta Faransa, da kuma dakatar da yarjejeniyar soji da ke tsakaninta da ƙasar Amurka.

Tun bayan juyin mulkin, Nijar ta fuskanci ƙarin hare-hare daga ƙungiyoyi masu iƙirarin jihadi da ke addabar yankin na Sahel.

 

Gwamnatin Adamawa ta dauki matakin kawo karshen rikicin manoma da makiyaya

Gwamnatin Adamawa ta dauki matakin kawo karshen rikicin manoma da makiyaya
Gwamnan Adamawa

Gwamnatin jihar Adamawa ta dauki wani muhimmin mataki na kawo karshen rikicin manoma da makiyaya a jihar.

A cewar sakataren gwamnatin jihar Auwal Tukur, gwamnatin ta yanke shawarar ganowa tare da samar da wuraren kiwo domin rage takun saka tsakanin kungiyoyin biyu.

An cimma wannan matsaya ne bayan wani gagarumin taron tsaro da Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya jagoranta, wanda ya hada hakimai da sarakunan gargajiya da shugabannin kansiloli.

Taron dai ya mayar da hankali ne kan magance tashe tashen hankula musamman a lokacin girbi.

Domin magance musabbabin rikice-rikicen, gwamnati ta yi shirin shirya tarukan karawa juna sani da taron karawa juna sani ga sarakunan gargajiya, tare da sanin rawar da suke takawa a cikin al’umma.

Wannan yunkuri na da nufin ilmantar da su a kan nauyin da ke kansu da kuma karfafa su don taimakawa wajen magance matsalolin tun da wuri.

Gwamnatin ta kuma bayyana makiyayan da ke kan iyaka a matsayin babban bangaren matsalar tare da shirin tantancewa da kuma yi wa duk makiyayan da ke kiwo a jihar rajista.

An yi kira ga al’umma da su taimaka wa gwamnati a kan wannan yunkurin, inda aka umurci shugabannin gargajiya da su fara taro don magance matsalolin da ke faruwa a kananan hukumominsu.

Bugu da kari, gwamnati ta himmatu wajen kara zuba jari a harkar noma, da yin amfani da fasahohin zamani don bunkasa abinci da kiwo.


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button