Nijar ta buƙaci Rasha ta saka hannun jari a fannin samar da ma’adinan Uranium
Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun buƙaci kamfanonin Rasha da su saka hannun jari a fannin samar da ma’adinan Uranium da sauran albarkatun ƙasa.
Ministan ma’adinan ƙasar Usman Abarshi, shi ya yi wannan kira a daidai lokacin da ake ci gaba da takaddama tsakanin Nijar da kamfanin Orano na ƙasar Faransa.
Kamfanin na Orano ya dakatar da fitar da sinadarin Uranium a ƙasar ne a watan da ya gabata yayin da dangantaka ta yi tsami tsakaninsa da gwamnatin mulkin sojin Nijar ɗin.
Ministan ya ce sun riga sun gana da kamfanonin ƙasar Rasha domin su zo su zuba jari a fannoni daban-daban.
Kalaman na minista na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasashe da dama ke yanke hulɗar dangantaka da Faransa, inda wasu suka ga Rasha da sauran ƙasashe.
Gwamnatin mulkin sojin Nijar ɗin ta sha alwashin yin garambawul ga dokokin da kamfanonin ƙasashen waje ke aiki da su wajen haƙo albarkatun uranium a ƙasar.
Tun da farko dai, kamfanin na Orano ya yi Alla-wadai da matakin janye masa izinin haƙar ma’adinai da gwamnatin mulkin sojin Nijar ta yi a watan Yuli, inda ya kasance ɗaya daga cikin manyan wurare da kamfanin yake aiki a duniya.