Najeriya da India sun jaddada aniyar tallafa wa juna ta fannonin tsaro da kasuwanci
Najeriya da India sun kara jaddada aniyar bunkasa kawance a tsakaninsu don karfafa alaka a fannoni da dama da suka hada da tattalin arziki da tsaro da harkar lafiya da samar da abinci.
Wannan na kunshe ne a sanarwar bayan taro ta hadin gwiwa da aka fitar a yau Lahadi a Abuja bayan kammala ziyarar da Firaministan Indiyar ya yi a Najeriya, wadda Shugaba Bola Tinubu ya gayyace shi.
A lokacin tattaunawar, shugabannin biyu sun amince su hada kai wajen yaki da ta’addanci da tabbatar da tsaro a teku da kuma musayar bayanan tsaro na sirri.
Firaminista Modi ya jaddada aniyar kasarsa ta taimaka wa shirin Najeriya na zamanantar da harkar tsaronta, inda ya nuna yadda kasarsa take abar amincewa a fannin kera makamai
Shugabannin biyu sun kuma nuna yadda kyakkyawar alakar kasuwanci tsakanin Najeriya da India, inda India take kasa mafi girma a alakara kasuwanci da Najeriya da kuma bayar da gagarumar gudummawa ga tattalin arzikin Najeriyar.
Najeriya ta yaba da gudummawar kamfanonin Indiya sama da 200 da ke aiki a cikinta, inda suka samar a ayyuka masu yawa da kuma damarmaki na zuba jari.
A fannin bunkasa harkokin kasuwanci da zuba jari kuwa shugabannin biyu sun umarci jami’ansu da su kammala dukkanin yarjeniyoyin da ke tsakaninsu a wannan fanni.
A bangaren samar da kayayyakin jin dadin jama’a kuwa sanarwar hadin gwiwar ta bayyana cewa India ta jaddada kudurinta na taimaka wa Najeriya ta hanyar bashi mai sassauci da taimaka mata da kwararru.