Na san masu hanu cikin binciken da EFCC ke yi mini –Okowa
Tsohon Gwamnan Jihar Delta, Dokta Ifeanyi Okowa, ya ce ya san mutanen da ke da hannu a binciken da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ta yi, inda ya ce baya tsoron binciken hukumar.
Okowa ya bayyana haka ne a wata ziyarar hadin kai da Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Jihar Delta, karkashin jagorancin Maj.-Gen. Felix Mujakperuo (mai ritaya), Orodje na Okpe, zuwa gidansa da ke Asaba ranar Alhamis.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC na tuhumar Okowa, wanda ya zama gwamna a karo na biyu, kan zargin karkatar da zunzurutun kudi har naira tiriliyan 1.3.
Tsohon gwamnan kuma dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023, ya bayyana zargin da ake yi masa a matsayin “mugunta da siyasa,” inda ya kara da cewa wasu mutane na yunkurin karkatar da bayanai domin biyan bukatunsu.
Okowa ya ce, “A siyasa, akwai abubuwa da yawa da mutum zai fuskanta, amma abin takaici ne idan aka gabatar da zarge-zarge marasa tushe ga manema labarai.”
Ya yi watsi da zargin karkatar da kudaden a matsayin “karya”
“Da’awar cewa wani zai iya yin almubazzaranci da irin wannan kudi yana nuna cewa za su rika karbar Naira biliyan 16 zuwa Naira biliyan 20 duk wata na tsawon watanni 96. Wannan ba kawai rashin hankali ba ne; yunkurin yaudara ne da gangan,” in ji Okowa.
Dangane da binciken da EFCC ta yi a baya-bayan nan, Okowa ya ce ya yi maraba da binciken da hukumar ke yi, kuma ya ga babu bukatar a dakile yunkurin ta.
“Bana tsoron duk wani bincike kuma ba zan hana EFCC gudanar da ayyukanta ba. Ba kamar sauran waɗanda ke neman umarnin kotu don hana bincike ba, na yi imani da gaskiya. Sai dai jama’a sun cancanci sahihan bayanai, ba wai kage na wasu mutane ba,” inji shi.
Okowa ya jaddada cewa zargin na siyasa ne kawai, inda ya kara da cewa cikin kwarin guiwa ya amsa dukkan tambayoyin jami’an EFCC.
“Bayanan da aka gabatar a cikin koken sun sha bamban da na gaskiya, kuma na tabbata masu binciken sun ga karyar. Na san tushen waɗannan hare-haren, amma ba za su hana ni ba. Na yi wa Jihar Delta hidima tare da goyon bayan jama’armu da shugabanninmu irinku, kuma mun samu gagarumin ci gaba,” ya shaida wa sarakunan gargajiya da suka ziyarce su.
Sarakunan gargajiyar dai sun yi alkawarin ba tsohon gwamnan goyon baya, tare da gode masa bisa kyakkyawar alakar da ya yi da su tare da bayyana kwarin gwiwar cewa adalci zai tabbata a gare shi.