Hatsarin mota ya yi sanadiyar rayuwar mutum 10 a Jigawa

Rundunar ƴansandan jihar Jigawa ta tabbatar da mutuwar mutum 10 a wani hatsarin mota a ƙauyen Yanfari da ke karamar hukumar Taura na jihar.

Spread the love

Lamarin wanda ya afku a yau Talata, 12 ga watan Nuwamba a daidai hanyar Kano-Hadejia, ya kuma janyo jikkatar wani fasinja ɗaya.

Kafar watsa labarai ta BBC Hausa ta ce a Wata sanarwa da kakakin ƴansandan jihar DSP Lawan Shiisu Adam, ya fitar, ya ce lamarin ya afku ne lokacin da wata motar ƙirar bas da ta fito daga jihar Kano zuwa Hadejia ɗauke fa fasinjoji 11, ta garu da wata tirela har ta kai suka jujjuya.

“Nan take direban motar tare da wasu fasinjoji tara da ya ɗauka suka mutu,” in ji sanarwar.

Bayan afkuwar lamarin, tawagar sintiri na ƴansandan reshen Taura suka garzaya wajen, inda suka ɗauki gawawwakin waɗanda suka mutu zuwa babban asibitin Hadejia.

Sun kuma ce sauran fasinja guda da ya jikkata na samun kulawa a cibiyar kiwon lafiya na Majia.


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button