Mutane Sama Da Dubu 25 Ne Suka Halarci Kallon Wasa Tsakanin Kano Pillars Da Heartland
Mutane Sama Da Dubu 25 Ne Suka Halarci Kallon Wasa Tsakanin Kano Pillars Da Heartland A Filin Wasa Na Sani Abacha Dake Kano A Jiya Lahadi
Magoya bayan Barcelona sun fusata saboda an bayyana yatsan lewandowski ne yayi satar gida.
Wakilin Neymar Pini Zahavi: “Babu wata tattaunawa da Neymar ke gudana domin barin Al Hilal.
Yana karkashin kwantiragin watanni 6 kuma yana farin ciki a kulab din. ”
“Ni da mahaifin Neymar, mu ne kawai za mu iya magana game da makomar sa. Ban san inda jita-jitar nan tafito a kwanan nan game da cewa zai koma Santos ba.
Manchester United ta nace wa matashin ɗanwasan Portugal Geovany Quenda, Gyokeres zai iya zama ɗanwasan United, Wojciech Szczesny zai ƙulla sabuwar yarjejeniya da Barcelona.
Eriksen zai bar Manchester United a ƙarshen kakar bana
Rahotanni na baiyana cewa dan wasan tsakiya na Manchester United da kuma Denmark, Christian Eriksen zai bar kungiyar a ƙarshen kakar bana.
Fabrizio Romano ne ya wallafa rahoton a shafinsa na X, inda ya ce a halin yanzu babu wata tattaunawa kan tsawaita kwantaragin Eriksen din a kungiyar ta United da ke buga gasar firimiya ta Ingila.
A 2022 ne Eriksen, mai shekaru 32 ya dawo Manchester United a kyauta.