Musiala ya ci wa Bayern ƙwallo a wasan St Pauli a Bundesliga

Spread the love

Jamal Musiala ne ya ci wa Bayern Munich ƙwallon da ta yi nasara a gidan St Pauli 1-0 ranar Asabar a Bundesliga, ta bai wa RB Leipzig tazarar maki shida.

Kafar BBC Hausa ta ruwaito cewar Ɗan wasan tawagar Jamus ya ci ƙwallon daga yadi na 30 a minti na 22 da take leda.

Ɗan ƙwallon tawagar Ingila, Harry Kane bai samu yin abin kirki ba a karawar, ya samu wata damar da ya buga tamaula ta yi saman raga.

Bayern ta kusan kara ƙwallo ta hannun Leon Goretzka da wanda Leroy Sane ya buga, amma mai tsaron ragar St Pauli, Nikola Vasilj ya sa ƙwazo.

Haka kuma Musiala ya yi kokarin kara ƙwallo na biyu daf da za a tashi a wasan na babbar gasar tamaula ta Jamus.

Leipzig za ta iya rage tazarar da ke tsakanintta da Bayern Munich, idan ta doke Borussia Monchengladbach ranar ta Asabar.


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button