Ministar Ilimi ta kaddamar da muhimman ayyuka 13 a cibiyar ilimin manya a Kano
Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya tare da haɗin gwiwar Kamfanin Maslaha Homes Ltd. ta kaddamar da samar da ayyuka 13 masu muhimmanci a Cibiyar Ilimin Manya da Dogaro da Kai (NMEC) da ke Farawa a Karamar Hukumar Kumbotso, Jihar Kano.
Da ta ke jawabi a wajen bikin aza harsashin aiyukan jarrabar cibiyar a Kano a jiya Juma’a, karamar Ministar Ilimi , Dakta Suwaiba Ahmad, ta bayyana cewa wannan aikin yana gudana ne karkashin tsarin haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da masu zaman kansu (PPP).
Ta bayyana cewa wannan aiki wani alkawari ne na gwamnati da nufin bai wa kowane ɗan Najeriya dama don samun ƙwarewa wajen rubutu da karatu da dogaro da kai daidai da ajandar “Sabon Fata” na Shugaba Bola Tinubu.
“Na yi matuƙar farin cikin aza harsashin aiyukan nan guda 13 da haɗin gwiwa tsakanin Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya da Kamfanin Maslaha Homes Ltd karkashin tsarin musayar filaye na haɗin gwiwa.
“Samar da ayyuka 13 masu muhimmanci a wannan cibiya ba kawai aiki ba ne kaɗai, alkawari ne na gwamnati da ta so ta yi tun tale-tale amma saboda rashin kudade isassu , sai aka samu jinkiri sai a wannan lokaci da shugaba Bola Tinubu zai yi”
Ta ce aiyukan sun hada da ajujuwa, wajen kwanan ɗalibai, dakunan koyon sana’o’i, dakin karatu da sauran gine-gine.
Ministar ta kuma ce a halin yanzu akwai ɗalibai kusan 800 da ke karɓar horo kan ƙwarewa daban-daban a cibiyar, inda ta ce wannan aiyuka za su kara yawan ɗaliban da yawan sana’o’in da za a rika koyar da su da nufin samun haɓakar tattalin arziki ga ƴan ƙasa.
A nashi ɓangaren, Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, wanda Kwamishinan Ilimi, Alhaji Umar Haruna Doguwa, ya wakilta, ya ce cibiyar NMEC tana da matuƙar muhimmanci wajen tarihin ilimi a Najeriya.
“Cibiyar an tsara ta don zama abin alfahari, wata cibiyar raya ilimin rubutu da karatu ga manya da ilimin bai daya a Najeriya da Afirka. Duk da haka, ci gaba ya kasance a hankali saboda ƙuntatawar albarkatu da wasu ƙalubale,” inji shi.
Haka kuma, Babban Sakataren NMEC, Farfesa Akapan Simon, ya bayyana cewa an tsara cibiyar don zama wata cibiyar horo ta yankin Afirka, wacce za ta ba mutane dama wajen samun ƙwarewa, ilimi da ƙarfin zuciya don inganta rayuwarsu.