Ministan wutar lantarki ya bada umarnin kafa kwamiti nan take domin duba matsalar wuta a kasar nan
Ministan wutar lantarki, Cif Adebayo Adelabu ya umarci Kamfanin rarraba wutar lantarki TCN da sauran hukumomin da abin ya shafa na ma’aikatar, da su fara aiwatar dasu kafa kwamiti domin magance matsalar rugujewar wutar lantarki a kasar.
Wannan na zuwa ne yayin da kamfanin rarraba wutar lantarkin ta yi kira da a samu fahimtar juna a tsakanin ‘yan Najeriya kan tabarbarewar wutar lokacin da aka fara aikin gyaran layin.
Umurnin daidaitawa na Ministan ya zo ne yayin da wani rahoto ya nuna cewa wutar na kasa ta samu matsala da misalin karfe 11:29 na safe, ranar Alhamis, 7 ga Nuwamba, 2024.
Mai bawa Ministan shawara na musamman kan dabarun sadarwa da yada labarai, Hon. Bolaji Tunji ya ruwaito Ministan yana cewa, dole ne dukkan hukumomin da abin ya shafa a ma’aikatar su tashi tsaye wajen aiwatar da shawarwarin da kwamitin ya gabatar a ranar Laraba 6 ga watan Nuwamba, 2024.
Shawarwari na kwamitin zai samar da dawwamammen mafita ga lalacewar lantarkin da ake ganin abin kunya ne a kasar nan, nan da cdogon lokaci,” in ji Bolaji.
A halin da ake ciki, hukumar ta rarraba wutar ta tabbatar wa masu amfani da wutar lantarki cewa ana ci gaba da kokarin tabbatar da samar musu da wutar lantarki ba tare da katsewa ba.
Sanarwar da Ndidi Mbah, Babban Manajan Hulda da Jama’a na kamfanin TCN ya fitar a ranar Alhamis, ya ce hukumar na kokarin tabbatar da cikakken aiki da shawarwarin kwamitin nan take, domin ceto Najeriya daga kara lalacewar wutar.
Kamfanin rarraba wutar lantarki ta TCN) na son sanar da jama’a cewa tashar samar da wutar na kasa ta samu matsala ne da misalin karfe 11:29 na safiyar yau, inda nan take aka fara kokarin farfado da ita, kuma a cikin mintuna kadan aka dawo da Axis na Abuja.
Matsalolin da aka fuskanta daya daga cikin tashoshin sadarwa na TCN ne ya haifar da matsalar, wanda dole ne a rufe shi don hana ci gaba da samun wasu matsalolin.