Ministan ilimi ya sauya tsarin shekaru 18 da ake bukata kafin shiga jami’a

Spread the love

Ministan ilimi ya sauya tsarin shekaru 18 da ake bukata don shiga jami’a

Dr. Morufu Olatunji Alausa, sabon Ministan Ilimi na Najeriya, ya sauya tsarin da magabacinsa Farfesa Tahir Mamman ya gindaya, inda ya bukaci dalibai su kai akalla shekaru 18 kafin su shiga jami’a.

 

Manufar da ta haifar da cece-kuce a tsakanin jama’a, Alausa ya yi la’akari da cewa sauya tsarin zai rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a fadin kasar. Da yake jawabi ga manema labarai a ranar Talata, Alausa ya bayyana cewa shekarun da ake bukata za su koma shekaru 16,

 

Majiyar TrustTV ta ruwaito cewa Da yake jaddada bukatar samar da ilimi mai amfani don magance karuwar rashin aikin yi, ya bayyana tsare-tsare na manyan makarantun da za su hada kai da makarantu masu zaman kansu don koyar da dalibai dabarun da za su dogara da su da kuma inganta ayyukan yi.

 

Alausa, wanda a baya karamin ministan lafiya ne, ya karbi mukamin ma’aikatar ilimi ne bayan wani sauyi da aka yi a majalisar ministocin kasa wadda ya yi sanadin ficewar wasu daga cikin ministocin.


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button