Matatar man Dangote ta rage farashin man fetur zuwa naira 899 kan kowacce lita

Matatar man Dangote ta rage farashin man fetur zuwa naira 899.50 a kan kowace lita.

Spread the love

Matatar man Dangote ta rage farashin man fetur zuwa naira 899.50 a kan kowace lita.

Matatar man Dangote ta rage farashin man fetur zuwa naira 899 kan kowacce lita
Dangote

An sanar da hakan ne a cikin wata sanarwa, a safiyar ranar yau Alhamis.

Matatar man Dangote ta ce an dauki matakin ne don samar da sauki ga ‘yan Najeriya kafin lokacin tafiya hutun karshen shekara. Daily trust

Matatar man Dangote ita ce ta farko mai zaman kanta a Afirka, wacce a baya ta rage farashin zuwa naira 970 kan kowace lita a ranar 24 ga Nuwamba, yanzu ta sanar da sabon farashin N899.50 kowace lita.

An tsara wannan ragi ne don sauƙaƙe farashin sufuri a lokacin bukukuwan karshen shekara, in ji sanarwar da Babban jami’in kula da sana’a da sadarwa, Anthony Chiejina ya sanya wa hannu.

Ya kara da cewa matatar man Dangote  ta kuma gabatar da wani tayi na musamman domin kara amfanar masu mu’amala da kamfanin.

Bugu da kari a hutun karshen shekara, matatar man Dangote na baiwa masu amfani da damar sayen karin litar man fetur a kan bashi ga kowace lita da aka siya akan kudi.

Don rage farashin sufuri a wannan lokacin hutu, matatar man Dangote tana ba da rangwamen hutu.

Daga yau matatar man Dangote yace farashin man fetur din zai kasance akan naira 899.50 akan kowace lita a wajen dakon manyan motocinmu.

Haka kuma, duk litar da aka saya a kan tsabar kudi, masu amfani za su samu damar siyan litar a kan bashi, tare da garantin banki daga bankin Access, First Bank, ko Zenith Bank, in ji Chiejina.

Matatar man Dangote ta kuma nuna jin dadin ta ga ‘yan Najeriya kan yadda suke ci gaba da ba da goyon baya a lokacin da kasar ke shiga lokacin bukukuwa.

Chiejina ya kara jaddada kudirin matatar man Dangote ya tabbatar da ‘yan Najeriya sun samu damar samun ingantattun kayyakin man fetur da suka dace da farashi, da kuma muhalli da injiniyoyi.

Ya kara da cewa, ayyukan matatar man Dangote sun kawo karshen Nijeriya kasancewar ta zama wurin jibge kayayyakin da ba su da inganci da ake shigo da su daga kasashen waje, wadanda ke haifar da babbar illa ga lafiyar dan Adam, injina, da muhalli. Matatar man Dangote.

Matatar man Dangote, tana tace ganga 650,000 a kowace rana, kuma ita ce matatar man Dangote na daya daga cikin matatu mafi girma a duniya.

Yana da cikakken ikon biyan 100% na ingantaccen kayan albarkatun man fetur na Najeriya, tare da ragi don fitarwa.

Ko kasafin kudin shugaba Tinubu zai iya farfaɗo da tattalin arzikin Najeriya?

Ko kasafin kudin shugaba Tinubu zai iya farfaɗo da tattalin arzikin Najeriya?
Kasafin kudi

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yi wa kasafin kuɗi na 2025 da ya gabatar a gaban majalisar dokokin ƙasar ranar Laraba take da Farfaɗowa domin tabbatar da zaman lafiya, da gina rayuwar ‘yan kasa.

Tinubu ya gabatar da kasafin na naira tiriliyan 47.9, wanda yafi na shekarar da ta gabata da kashi 36.8 cikin 100. Kasafin shine na biyu da Tinubu ya yi tun bayan rantsar da shi a matsayin shugaban kasar a watan Mayun 2023.

An dai ɗora kasafin kuɗin na 2025 ne a kan dala 75 a kan kowacce gangar ɗanyen mai guda kuma ana sa ran Najeriyar za ta samar da gangar ɗanyen man fiye da miliyan biyu duk rana a shekarar mai kamawa.

Shugaba Bola Tinubu ya shaida wa majalisun dokokin cewa suna fatan samun naira tiriliyan 34.82 ta hanyar kuɗin shiga domin zuba wa a kasafin.

Sai dai kuma ya ce kasafin na da giɓin naira tiriliyan 13.08 wato kashi 3.08 cikin 100 na jimillar kasafin, yayin da ake hasashen gwamnatin za ta ciyo bashin tiriliyan 13 a cikin gida da waje domin cike giɓin.

A cikin jawabinsa, shugaba Tinubu ya ce tattalin arziƙin Najeriya ya samu haɓaka da kashi 3.46 cikin 100 a kaso na uku cikin huɗu na shekarar 2024, fiye da 2.54 a irin wannan lokacin a 2023.

Ya ƙara da cewa asusun Najeriya a ƙasar waje yanzu ya kai kusan dala biliyan 42, wanda ya samar da kariya daga duk wata komaɗar tattalin arziƙi da ka iya tasowa.

Sai dai masana tattalin arziƙi a Najeriya na ganin babu wani tabbas ko kasafin kudin zai iya farfado da tatattalin arziƙin ƙasar kamar yadda gwamnatin ta Tinubu ke so ‘yan ƙasa su amince.

Kasancewar tattalin arziƙin Najeriya na cikin rashin lafiya, yana kuma samun koma-baya a kowane lokaci, in ji Dr Murtala Abdullahi Ƙwara masanin tatattalin arziƙi na Jami’ar Umaru Musa Ƴar’adua da ke jihar Katsina.

Ya ƙara da cewa da wuya kasafin kudin na 2025 ya iya farfado da tattalin arziƙin Najeriya. Idan aka kalli alƙalumman da ake da su a ƙasa za a iya cewa da kamar wuya.

Wasu alƙaluman da aka sanya cikinsa abu, da yawansu ba haka suke ba a harkar tatattalin arziƙi ta zahiri. Farashin dala da kuma yadda ake sayar da mai a yanzu da kuma adadin man da ake iya haƙowa a yanzu, duka hasashe ne kawai.

Dr. Ƙwara ya ce hasashen da aka yi cikin kasafin kuɗi kan canjin dalar Amurka kan N1,400, zai yi wahala a iya samun haka saboda idan aka yi la’akari da farashin da yanzu dalar take kai, kuma ba ta fara yin ƙasa ba duk da cewa an kusa shiga shekarar.

Ko me zai faru idan aka kasa cim ma hasashen da aka yi?

Abin da zai faru shi ne, za a iya rasa damar aiwatar da kasafin kuɗin, wato duk abin da aka ce za a yi da kasafin kuɗin ba za a yi ba har sai an sake nemo hanyar da za a cike giɓin, ko da ta hanyar ciwo bashi ne, a cewar Dr. Ƙwara.

Masanin ya ce Najeriya ta jima cikin ƙangin bashi. Amma ya ce ba kowane bashi ne yake zama illa ba, yana mai cewa ya danganta da yadda aka yi amfanin da kudin da aka ciyo bashin.

To mece ce matsalar Najeriya game da bashin?

Matsalar Najeriya ita ce, ba a yin abin da ya dace da kudin da ake amsowa idan aka yi la’akari da ƙididdigar da ake da ita. Misali, me ya sa za ka ciwo bashi saboda saya wa ƴan majalisa motoci ko kuma wasu abubuwa?

Gwamnan Kebbi ya gabatar da kasafin kudi naira biliyan 580.32 na shekarar 2025

Gwamnan Kebbi ya gabatar da kasafin kudi naira biliyan 580.32 na shekarar 2025
Gwamnatin Kebbi

A ranar Larabar da ta gabata ne Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya gabatar da daftarin kasafin kudi na naira 580,327,469,380 na shekarar 2025 ga majalisar dokokin jihar.

Gwamnan ya ce an ware naira biliyan 453 don manyan ayyuka, yayin da aka ware naira biliyan 127 don kashe kudade gudanarwa na yau da kullum.

Yakara da cewa, kasafin wanda aka masa lakabi da Budget of Economic and Infrastructural Consolidation, wanda ake nufin bunkasa tattalin arziki da inganta ababen more rayuwa a fadin jihar kuma an tsara shi ne kan kudaden shigar da aka yi hasashen zai kai N235.2bn daga asusun kasafi na tarayya da kuma naira biliyan 26 da ake samu a cikin gida.

Gwamnan ya shaida wa majalisar cewa gwamnatinsa na shirin gyara hanyar Koko/Mahuta da N41bn saboda kudaden shigar da jihar ke samu ya karu da kashi 40 cikin 100, daga naira biliyan 8 zuwa 11.

Anasa martanin da mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Mohammed Samaila Bagudo ya mayar, ya tabbatar wa gwamnan jihar cewa wannan kudirin zasuyi nazari cikin gaggawa tare da amincewa da kasafin kudin.

 


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button