Mataimakin shugaban kasa Shettima ya buƙaci shugabanni su yi riqo da gaskiya

Spread the love

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya yi kira ga ‘yan Nijeriya, musamman shugabanni, da su yi koyi da shugabanci na gaskiya, ta hanyar fifita hidimtawa al’umma don gina kasa.

Ya bukaci ’yan Najeriya da su fifita ayyukan ibada da fiye da bukatun kansu a wannan zamani.

Da yake jawabi a ranar Juma’a a yayin bude babban masallacin Ibapon da ke garin Ogbomoso na jihar Oyo, mataimakin shugaban kasar ya nuna damuwarsa kan yadda al’umma ke bijirewa dokokin Allah su ke aika ta abinda bai dace ba.

A cewarsa, masallacin, da Sanata Abdulfatai Omotayo Buhari mai wakiltar mazabar Oyo ta Arewa ya gina, ya yi shine saboda Allah domin samun saka mako mai kyau ranar gobe kiyama.

Tun da farko da ya ke jawabi mataimakin shugaban majalisar dattawa Sanata Barau Jibrin, ya jinjina wa Sanata Buhari, inda ya ce aikin masallacin ba hidima ne ga al’ummar jihar kadai ba, har ma ga al’umma musulmai baki daya.

Da yake mayar da martani, Sanata Buhari ya ce hakika abin alfahari ne a gare shi ya kammala aikin Masallacin.

Ya mika godiya ta musamman ga Mataimakin Shugaban Kasa, Gwamnonin Jihohin Oyo da Kwara, da ‘yan Majalisar Dokoki ta Kasa, da sauran al’umma da suka bayar da gudunmawa wajen ganin an samu nasarar a aikin gina masallacin.


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button