Masu kasuwar man fetur sun ki amincewa da da’awar matatar Dangote.

Spread the love

Daily Trust Kungiyar dillalan man fetur ta Najeriya (DAPPMAN) ta karyata ikirarin da matatar Dangote ta yi a baya-bayan nan na cewa duk wani dan kasuwar mai da ya shigo da man fetur a farashi kasa da na matatar baida inganci.

Matatar ta yi zargin cewa wadannan kayayyaki da ake shigowa da su sun hada da baki da ‘yan kasuwa na kasa da kasa wajen shigar da mai maras inganci a Najeriya.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin, Babban Sakatare na DAPPMAN, Olufemi Adewole, ya musanta wadannan ikirari, yana mai tabbatar da cewa mambobinta sun himmatu wajen aiwatar da kyawawan dabi’u da kuma yi wa ‘yan Najeriya hidima da gaskiya. “Mambobinmu a bangaren man fetur na kasa sun sadaukar da kansu don kara kima, ba yaudarar mutane ba”. in ji Adewole, yana mai jaddada kudirin ‘yan kungiyar ta DAPPMAN na kiyaye kyawawan halaye da akansata dashi.

Ya kuma yi bayanin cewa farashin man fetur a duniya yana tashi ne bisa la’akari da yanayin kasuwa daban-daban, kuma DAPPMAN ta kididdige yawan kudin saukar sa a fili, tare da ka’idojin farashi ga jama’a. Kudin shigo da kaya yana nuna karfin kasuwa, ba wai sabawa ka’ida ba,” in ji Adewole, yana mai zargin rashin gaskiya a matatar Dangote a tsarin farashin ta, wanda aka nisantar da jama’a har ya zuwa yanzu.

Adewole ya kuma bayyana mamakinsa da sanarwar da matatar ta yi cewa tana da tarin litar man fetur miliyan 500. “Idan akwai irin wannan ajiyar, ya kamata a sanar da ‘yan kasuwa da farko,” in ji shi.

Da yake jaddada kudirin DAPPMAN na yin adalci, Adewole ya ce, “Matsayinmu a bayyane yake: za mu ci gaba da gudanar da aiki bisa ka’ida, tare da bayar da shawarwarin samar da daidaito a fannin gaskiya da gaskiya ba tare da son rai ba ko kuma son zuciya.


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button