Masu bautar kasa sun bukaci a aiwatar da alawus dinsu na naira dubu 77
Mambobin kungiyar masu yi wa kasa hidima ta kasa sun bukaci gwamnatin tarayya da ta aiwatar da kudirin bayar da alawus na Naira 77,000 domin rage musu wahalhalun da suke ciki.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewar mambobin sun ce duk da amincewar gwamnatin tarayya na sabon mafi karancin albashi a watan Yulin 2024, mambobin kungiyar na ci gaba da karbar tsohon alawus na N33,000.
A cewarsu, tsohon alawus din ba ya biya musu bukatun su musamman na tafiye tafiye, abinci, da sauran bukatu na yau da kullun.
‘Yan kungiyar sun yi amfani da kafafen sada zumunta na zamani don bayyana damuwarsu a ranar Laraba.
Mambobin kungiyar dai sunyi amfani da kafafen sada zumunta na zamani irin X, facebook da sauransu wajen bayyana irin halinda suke ciki.
Kamfanin dilancin labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta amince da sabon mafi karancin albashin ma’aikata bayan karewar tsohon tsarin albashin a watan Afrilu. Inda ake sa ran za a mika sabuwar dokar amincewar karin kudin alawas din ga mambobin kungiyar.