Masu aikata laifin kone-kone, da kwasar ganima muka kama – Kayode
Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya, Mista Kayode Egbetokun ya ce sabanin abinda wasu kungiyoyi ke yadawa a kafafen yada labarai, rundunar ‘yan sandan Najeriya ba ta kama wani karamin yaro da ya yi zanga-zanga a lokacin zanga-zangar tsadar rayuwa ba, maimakon haka ‘yan sanda sun kama wasu masu laifi, wadanda suke tabka kone-kone, na kadarori, wuraren jama’a, kutsawa tare da wawushe kayan shaguna, manyan kantuna, da dai sauransu.
Ya kuma bayyana cewa, ‘yan sandan da aka samu suna bayar da aikin rakiya ga ‘yan kasashen waje (’yan China da Malaysia 100) da aka kama bisa laifin aikata laifuka ta yanar gizo da damfara a Abuja, suna gudanar da ayyukan da ba bisa ka’ida ba, kuma an kama su saboda “ba a tura su a hukumance ba. An tsare su a gidan yari kuma za a hukunta su kamar yadda doka ta tanada.”
Sufeton ya bayyana haka ne a wani taron karawa juna sani na “Haba Kwarewa kan Laifuka” da aka gudanar ga shugabannin sassan binciken ‘yan sanda da na leken asiri a fadin kasar nan a cibiyar ‘yan sanda da ke Abuja.
Egbetokun ya ce: “Da farko ina so in gode wa shugaban kasa Bola Tinubu bisa jajircewarsa na uba wajen bayar da umarnin a sako duk wadanda aka kama. Amma bari in gyara wani ra’ayi, babu wani, ciki har da wani ƙarami da aka kama saboda fara zanga-zangar rashin shugabanci. Mun samar da tsaro daga masu zanga-zangar saboda mun ce suna da hakkin yin zanga-zanga.
“Wadanda aka kama ɓarayi ne da suka shiga cikin shaguna suna kwasar ganima. Wadanda suka yi ta kona kadarori da kayayyakin jama’a su ne wadanda muka kama.
“Wadanda ake zargin sun kasance masu laifi da aka kama a lokacin zanga-zangar. An dai dauki hotonsu a bidiyo suna ta kone-kone, tare da lalata dukiyoyin jama’a. Mun ga a bidiyo, da barnatar da kadarorin jama’a, da sace-sacen manyan shagunan kasuwanci da kona wuta.”
Da yake gargadin cewa jami’an ‘yan sandan da suka yi watsi da binciken za su fuskanci takunkumi, sufeton ya ce: “Duk wani jami’in da aka samu yana son cin mutuncin sashen binciken mu za a hukunta shi. Inji shi.
Ya kara da cewa “Jami’an da ake zargin sun kama kananan yara ba za a hukunta su ba saboda sun kama masu laifi, ba masu zanga-zanga ko kananan yara ba,” in ji shi.