Mako daya ya rage wa’adin mulki na ya kare EFCC ta gayyatace ni – Obaseki
Gwamna Godwin Obaseki na Jihar Edo ya ce ya samu labarin kama shi da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati ta (EFCC) ta yi a mako daya da wa’adin mulkin sa zai cika.
Gwamnan, ya ce ba ya tsoron duk wani kamawa da binciken da hukumar za ta yi akan gwamnatinsa kan “korafe-korafen da ya ambata da wasu “mugaye da miyagu” suka rubuta a kanshi don cin zarafi da cutar da shi.
A cewar jaridar THISDAY, Obaseki yayi wannan maganar ne yayin wani taro a Abuja ranar Alhamis
Obaseki, wanda ya rike mukamin gwamnan Edo tun a shekarar 2016, ya ce zai shafe lokacinsa a hannun hukumar ta EFCC yana gudanar da bincike da nazarce-nazarce.
Gwamnan ya ce duk inda hukumar ta suka ajiye shi zai zauna saboda yasan abinda ya yi a jihar sa ta Edo zai za ma abin koyi ga sauran alummar jihar.