Majalisar Wakilai ta buƙaci CBN ya dakatar da yi wa ma’aikata 1,000 ritaya
Majalisar wakilai ta bukaci Babban Bankin Najeriya (CBN) da ya dakatar da shirin ritayar ma’aikata 1,000.
Majalisar wakilai ta bukaci Babban Bankin Najeriya (CBN) da ya dakatar da shirin ritayar ma’aikata 1,000.
A cewar rahotanni, babban bankin ya shirya tsaf don ritayar ma’aikatan tare da samar musu da kudin fansho da ya kai sama da naira biliyan 50.
A zaman majalisar da aka yi ranar Talata, majalisar ta yanke shawarar kafa kwamitin wucin gadi domin binciken tsari da halaccin wannan aikin, tare da tabbatar da gaskiya, adalci, da kuma yin amfani da kudade yadda ya kamata.
Majalisar ta dauki wannan matakin ne bayan amincewa da kudurin gaggawa da Kama Nkemkama daga Jihar Ebonyi ya gabatar.
An amince da kudurin ne ta hanyar kada kuri’ar baki da Tajudeen Abbas, kakakin majalisar, ya jagoranta.
Saboda haka, majalisar ta bukaci ma’aikatar kwadago da ayyuka da ta kare hakkokin ma’aikatan da abin ya shafa.
Daily Nigerian Hausa ta ruwaito cewar Kwamitin da za a kafa yana da makonni hudu don gudanar da bincike tare da gabatar da rahoto ga majalisar.
Majalisar Wakilai ta bankaɗo Kwalejin Kimiyya mai ɗalibai 142 da ma’aikata 154 amma aka kashe N600m
Kwamitin Majalisar Wakilai kan Kwalejojin Kimiyya da sauran manyan makarantu ya gano cewa sabuwar Kwalejin Kimiyya ta Tarayya da ke Ugep, Jihar Cross River, na da dalibai 142 kacal tare da ma’aikata 154 na koyarwa da marasa koyarwa.
Kwalejin ta kashe kusan Naira miliyan 600 kan albashi da sauran kudaden gudanarwa, tare da kashe wani karin Naira miliyan 38 kan tafiye-tafiyen cikin gida.
Wannan gaskiya ta bayyana ne yayin da shugaban kwalejin, Farfesa Edward N. Okey, ya jagoranci shugabannin makarantar zuwa Majalisar a wani bincike na duba ayyukan da ke gudana.
A ci gaba da binciken da Kwamitin ke yi kan cibiyoyin ilimi karkashinsu, an gayyaci Kwalejojin Kimiyya na Tarayya da wasu cibiyoyin fasaha daga yankin Kudu maso Kudu, ciki har da Kwalejin Kimiyya ta Tarayya, Orogun; Kwalejin Kimiyya ta Tarayya, Ugep; Kwalejin Kimiyya ta Man Fetur da Gas, Bonny; Kwalejin Kimiyya ta Tarayya, Auchi; Kwalejin Kimiyya ta Tarayya, Ekowe; Kwalejin Kimiyya ta Tarayya, Ukana; da kuma Cibiyar Gudanar da Fasahar Gina Gine, Uromi.
Shugaban Kwamitin, Fouad Laguda (APC, Legas), tare da sauran mambobin kwamitin, sun bayyana bacin ransu kan yadda Kwalejin da aka kafa a 2021 ke kashe makudan kudade don gudanarwa ga dalibai 142 kacal.
A bayanin da shugaban kwalejin ya gabatar a gaban Kwamitin, ya ce an yi amfani da Naira biliyan 2 da aka ba su a matsayin kudin fara aiki wajen gyara tsohon Ginin Makarantar Sakandare ta Al’ummar Ugep da aka yi watsi da ita don zama rikon kwarya, yayin da suke gina gine-ginen da suka karbe a Cibiyar Gudanar da Fasahar Kere-Kere (ITM) da yanzu ya zama sabon shalkwatar kwalejin.
Labarai masu alaƙa
Zazzafar muhawara ta kaure a zauren majalisar kan dokar haraji