Majalisar Wakilai ta bankaɗo Kwalejin Kimiyya mai ɗalibai 142 da ma’aikata 154 amma aka kashe N600m
Kwamitin Majalisar Wakilai kan Kwalejojin Kimiyya da sauran manyan makarantu ya gano cewa sabuwar Kwalejin Kimiyya ta Tarayya da ke Ugep, Jihar Cross River, na da dalibai 142 kacal tare da ma’aikata 154 na koyarwa da marasa koyarwa.
Kwalejin ta kashe kusan Naira miliyan 600 kan albashi da sauran kudaden gudanarwa, tare da kashe wani karin Naira miliyan 38 kan tafiye-tafiyen cikin gida.
Wannan gaskiya ta bayyana ne yayin da shugaban kwalejin, Farfesa Edward N. Okey, ya jagoranci shugabannin makarantar zuwa Majalisar a wani bincike na duba ayyukan da ke gudana.
A ci gaba da binciken da Kwamitin ke yi kan cibiyoyin ilimi karkashinsu, an gayyaci Kwalejojin Kimiyya na Tarayya da wasu cibiyoyin fasaha daga yankin Kudu maso Kudu, ciki har da Kwalejin Kimiyya ta Tarayya, Orogun; Kwalejin Kimiyya ta Tarayya, Ugep; Kwalejin Kimiyya ta Man Fetur da Gas, Bonny; Kwalejin Kimiyya ta Tarayya, Auchi; Kwalejin Kimiyya ta Tarayya, Ekowe; Kwalejin Kimiyya ta Tarayya, Ukana; da kuma Cibiyar Gudanar da Fasahar Gina Gine, Uromi.
Daily Nigerian Hausa ta ruwaito cewar Shugaban Kwamitin, Fouad Laguda (APC, Legas), tare da sauran mambobin kwamitin, sun bayyana bacin ransu kan yadda Kwalejin da aka kafa a 2021 ke kashe makudan kudade don gudanarwa ga dalibai 142 kacal.
A bayanin da shugaban kwalejin ya gabatar a gaban Kwamitin, ya ce an yi amfani da Naira biliyan 2 da aka ba su a matsayin kudin fara aiki wajen gyara tsohon Ginin Makarantar Sakandare ta Al’ummar Ugep da aka yi watsi da ita don zama rikon kwarya, yayin da suke gina gine-ginen da suka karbe a Cibiyar Gudanar da Fasahar Kere-Kere (ITM) da yanzu ya zama sabon shalkwatar kwalejin.
Naira 25,000 ake bamu a matsayin kudin wata – Hukumar Yaki da Cutar Kanjamau ta Jihar Yobe
Babban Sakataren Hukumar Yaki da Cutar Kanjamau ta Jihar Yobe (YOSACA), Dokta Jibrin Adamu Damazal, ya ce rashin isassun kudade na daya daga cikin manyan kalubalen yaki da cutar kanjamau a jihar.
Da yake jawabi yayin wani taron da aka gudanar a gidan gwamnati da ke Damaturu don bikin ranar yaki da cutar kanjamau ta duniya 2024, Dakta Damazal ya bayyana cewa hukumar na karbar Naira 25,000 kacal a matsayin kason wata-wata, wanda ya bayyana a matsayin rashin wadatuwa wajen biyan bukatun aiki.
Ya jaddada cewa, kara yawan kudaden zai baiwa kungiyar YOSACA damar fadada shirye-shiryen da suka shafi marasa galihu kamar yara, matasa, da mata, da kuma tabbatar da dorewar kokarin yaki da cutar kanjamau
Mataimakin Gwamna Mai Mala Buni, wanda ya wakilci Gwamna Idi Barde Gubana ya jaddada kudirin gwamnatin jihar na yaki da cutar kanjamau.
Akalla mutane 2,934 ne ke dauke da cutar kanjamau a halin yanzu a fadin kananan hukumomi 13 na jihar Nasarawa, wanda hakan ya nuna an samu raguwa daga mutane 4,222 a shekarar 2023 da kuma 6,614 a shekarar 2022.
Babbar Daraktar Hukumar Yaki da Cutar Kanjamau ta Jihar Nasarawa (NASACA), Dakta Ruth Nabe-Bello, ce ta bayyana hakan a ranar Litinin din da ta gabata a yayin taron ranar yaki da cutar kanjamau ta duniya na shekarar 2024 a Lafia, babban birnin jihar.
Ta bayyana damuwarta game da kyama da nuna wariya da masu dauke da cutar kanjamau ke fuskanta a jihar, inda ta ce takaita hanyoyin samun kiwon lafiya musamman ga manyan al’umma, ya kasance wani lamari mai daukar hankali.
Wike zai kaddamar da gina hanyoyi 4, wasu yankuna a Abuja
Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, a wannan makon zai kaddamar da wasu sabbin tituna guda hudu, da wuraren kula da ma’aikatan makarantar koyon aikin lauya ta Najeriya, da sauran ayyuka.
Babban mataimaki na musamman ga Ministan Sadarwa da Sabbin Kafafen Yada Labarai na babban birnin tarayya, Lere Olayinka, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, inda ya ce za a kaddamar da sabbin ayyuka guda shida tsakanin wannan mako zuwa mako mai zuwa.
Ya ce za a kuma raba sabbin motoci ga jami’an tsaro domin inganta ayyukansu.
Ya zayyana wasu daga cikin ayyukan da za a kaddamar da su sun hada da gina titin Kabulsa-Takushara, gina titin Kabusa-Ketti, samar da hanyar shiga sabon filin makarantar EFCC da ke gundumar Giri da kuma zane; gini da inganta hadadden ofishoshi
“Sauran kuma sun hada da zane tare da gina rukunin ma’aikata 10 na Makarantar Lauyoyi ta Najeriya da ke yankin Bwari da kuma gina titin kilomita 15 daga A2 Junction Abuja zuwa Lokoja zuwa Pia a karamar hukumar Kwali.
Labarai masu alaƙa
Zazzafar muhawara ta kaure a zauren majalisar kan dokar haraji