Zazzafar muhawara ta kaure a zauren majalisar kan dokar haraji
Haraji: Yadda zazzafar muhawara ta kaure tsakanin Barau Ndume a majalisa kan kudurin dokar haraji na Tinubu
Yadda zazzafar muhawara ta kaure tsakanin Barau Ndume a majalisa kan kudurin dokar haraji na Tinubu
An samu takaddama mai zafi a majalisar dattawa yayin da Sanata Ali Ndume ya yi martani ga Mataimakin Shugaban Majalisar, Barau Jibrin, kan kokarin gayyatar kwararru kan haraji da jami’an gwamnati zuwa zauren majalisa ba tare da sanarwa ba.
Jaridar Daily Nigerian Hausa ta ruwaito cewar Rikicin ya ta’allaka ne kan Dokokin Gyaran Haraji, inda wasu ƴan majalisa daga yankin arewa suka bayyana rashin amincewarsu.
Rikicin ya fara ne lokacin da Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisar, Opeyemi Bamidele, ya sanar da wani ba-zata game da dakatar da ajandar ranar don bai wa kwararrun haraji da jami’ai, ciki har da Shugaban Hukumar FIRS, damar gabatar da jawabi ga ‘yan majalisa kan Dokokin Gyaran Haraji da ake takaddama kansu.
Duk da haka, Sanata Abdul Ningi ya nuna adawa da hakan bisa ka’idojin Majalisar Dattijai. Ya ce ka’idojin ba su ba da izini ga kowa ya yi magana a zauren majalisa ba sai tsoffin Shugabannin Kasa, tsoffin Shugabannin Majalisar Wakilai, da tsoffin sanatoci.
Ningi ya jaddada cewa irin wannan bayani daga kwararru ya dace a yi shi ne a matakin kwamitocin majalisa, ba a taron majalisar gaba daya ba, kasancewar dokokin majalisar ba su amince da irin wannan ba.
Sanata Barau Jibrin, wanda ke jagorantar zaman majalisa, ya mayar da martani ta hanyar cewa Dokokin Gyaran Haraji suna da muhimmanci ga kasa kuma tuni Majalisar Wakilai ta yi aiki a kansu.
Ya yi bayanin cewa bai wa kwararru damar yin magana a zauren majalisar zai taimaka wa ‘yan Najeriya su fahimci abinda dokokin suka kunsa. Daga nan sai ya yi fatali da maganar Ningi.
Sanata Ndume, cikin bacin rai, ya fada wa shugaban zaman majalisar da cewa, “Za ku iya cimma muradinku, amma ni zan yi magana.” Ya kuma kara da cewa, “Za ku iya amfani da guduma, amma ni zan yi amfani da muryata.”
Rikicin ya dada ta’azzara lokacin da Sanata Ndume, cikin takaici, ya jagoranci wasu ‘yan majalisa daga arewa wajen ficewa daga zaman majalisar a matsayin alamar rashin jin dadi game da take dokar majalisa.
Bayan roko daga Shugaban Marasa Rinjaye da wasu abokan aikinsa, Ndume da sauran sanatocin da suka fita suka koma zauren majalisa.
Da suka dawo, Ndume ya sake daukar mataki ta hanyar yin magana bisa ka’ida, yana neman Mataimakin Shugaban Majalisa Barau ya ba shi hakuri saboda zarginsa da yin magana ba tare da hujja ba.
Amma Barau ya sake yi masa fatali da maganarsa, sannan aka ci gaba da bai wa kwararrun haraji damar yi wa sanatoci bayani kan Dokokin Gyaran Haraji, duk da adawar da aka yi.
Ko majalisa za ta amince da sabuwar dokar harajin da ke tayar da ƙura a Najeriya 2024
Ƙudurin dokar da ta shafi harajin na ci gaba da tayar da ƙura a Najeriya inda wasu bayanai ke cewa shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu na ci gaba da kamun ƙafa ga ƴan majalisar dokokin ƙasar domin ganin sun amince.
Bayanai na cewa shugabannin majalisun na ci gaba da wani zaman tattaunawa domin shawo kan sauran ƴan majalisar su amince da kudurin dokar, wanda shugaban kasa ke neman a gaggauta domin ta soma aiki daga ranar 1 ga watan Janairun 2025.
Sai dai ƴan adawa da wasu shugabanni musamman daga shiyar arewa na ganin dokar tamkar wani yankan baya ne na neman jefa yankinsu cikin karin wani kuncin talauci.
Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta ce tana son tabbatar sabon tsarin harajin daga cikin cikin matakan da take ɗauka na saita tattalin arzikin kasar duk da shawarar majalisar kula da tattalin arzikin Najeriya na dakatar da kuɗirin.
Yanzu kallo ya koma kan ƴan majalisa ko za su amince da kudirin dokar harajin da ake ci gaba da cecekuce?
Gwamnati ta ce babban dalilin sabuwar dokar harajin shi ne sake fasalin yadda ake karɓar harajin domin kawo ƙarshen ƙalubalen da gwamnati ke fuskanta kamar harajin birane daban-daban, rage nauyin harajin daga kan ɗaiɗaikun ‘yan ƙasa da kasuwanci tare da taimakwa wajen kasuwanci domin samar da tattalin arziki da makoma mai kyau ga Najeriya.
Sai dai ƴan’adawa kamar Alhaji Buba Galadima jigo a jam’iyar NNPP ya ce suna kallon dokar ne kan cewa ƴan Najeriya sun hau kan siradi, “Allah kadai zai iya kuɓutar da mu sai ƴan majalisa da muka zaɓa.”
Buba Galadima ya ce an matsawa ƴan majalisar lamba, “Ana amfani da dukkan wata dama, har da ta kuɗi don a shawo kan su, su tabbatar da wannan doka, wadda za ta cutar da al’ummar Najeriya ba ƴan arewa kaɗai ba.”
“Duk ɗan majalisar da ya goyi bayan wajen tabbatar da wannan doka to maƙiyin al’ummarsa ne,” cewar Buba Galadima.
BBC Hausa ta rawaito cewa, Tuni dai gwamnonin jihohi arewa suka bayyana adawarsu da kudurin, tare da yin umarni ga wakilan yankin a majalisar tarayya su yi watsi da kudirin.
Rikicin kan harajin VAT tsakanin jihohi da gwamnatin tarayya ya haifar da wasu manyan hukunce-hukuncen kotu da wasu da har yanzu ake shari’arsu.
Rashin ambatar harajin VAT a kundin tsarin mulkin 1999 ya ƙara rikita lamarin wanda hakan ya haifar da gibi. Bincikenmu ya gano tattara harajin a tarayya ya fi sauki da alfanu.
Da zarar an shawo kan taƙaddamar da ake yi, za a sanya batun VAT a tsarin mulki.
Yadda ake raba shi a yanzu tarayya 15 jihohi kashi 50 sai kuma ƙananan hukumomi kashi 35 zai dakata zai koma tarayya 10 jihohi 55 sai kuma ƙananan hukumomi kashi 35 cikin 100.
Daya daga cikin abubuwan da ke janyo cecekuce a kudurin dokar shi ne batun harajin da ake cirewa daga kuɗin da mutum ke samu wato Personal Income Tax a Turance.
A sabon ƙudurin dokar, an sake fasalin harajin da ake cirewa daga aljihun jama’a inda gwamnatin tarayya ta yi iƙirarin cewa za a ɗauke nauyin haraji daga kan masu ƙaramin ƙarfi.
Ƙudurin dokar dokar ya ce ba za a buƙaci mutanen da ke samun kudaden da suka yi kasa da naira 800,000 a shekara su biya haraji kan wadannan kudaden ba, har sai kuɗn da ake samu a shekara ya kai milaiyan 2.2 kafin ya fara biyan harajin kashi 15 cikin 100 a kai.
Za mu sake gabatar da kudurin da aka ƙi a kan wa’adin shekaru 6-majalisar wakilai
Mambobin Majalisar Wakilai 34 da suka dauki nauyin kudirin yi wa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima na shekarar 1999 don samar da wa’adin mulki na shekara shida ga shugaban kasar sun yanke shawarar sake gabatar da kudirin.
Dan majalisar wakilai Ikenga Ugochinyere (PDP-Imo) ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Juma’a, biyo bayan kin amincewa da kudirin dokar a ranar 21 ga watan Nuwamba yayin zaman majalisar.
Labarai masu alaƙa
An bukaci Majalisar Dattijai ta yi watsi da kudurin dokar hukumar kula da ma’adanai ta Najeriya
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya nan news ya ruwaito cewa kudirin dokar ya bukaci a gabatar da wa’adin mulki na shekara shida ga shugaban kasa, gwamnoni, da shugabannin kananan hukumomi.
NAN ta kuma ruwaito cewa, kudirin ya bukaci a sauya shiyya-shiyya na kujerun shugaban kasa da na gwamnoni, da kuma gudanar da dukkan zabuka a rana daya.
Sai dai Ugochinyere, ya ce duk fata ba a rasa ba a kan kudirin, domin za a kara yin shawarwari.
Dan majalisar wanda shi ne jagoran da ya dauki nauyin kudirin dokar, ya ce matakin da aka dauka a zauren majalisar ba zai kawo karshen tashe-tashen hankula da fata ba, inda ya ce za a cimma manufar da aka sanya a gaba.
“Gwagwarmaya na sake fasalin tsarin mulkin dimokuradiyyar mu ta zama mai tattare da kowa da kuma samar da hanyar tabbatar da adalci, daidaito da kuma gaskiya ba a rasa ba.
“Shawarar da aka yanke a zauren majalisar a jiya (Alhamis) na kin amincewa da kudirin na wa’adin mulki na shekara shida da kuma gudanar da duk zabuka a rana daya ba zai kawo karshen tashe-tashen hankula ba,” inji shi.
3 Comments