Macron ya tarbi Tinubu a kasar Faransa
A ranar Alhamis din nan ne shugaba Bola Tinubu ya fara ziyarar kwanaki biyu a kasar Faransa, inda bangarorin biyu ke neman karin hadin gwiwa a fannin tattalin arziki.
Sannan kuma birnin Paris na neman habaka alaka a nahiyar Afirka da ke magana da turancin Ingilishi, sakamakon koma bayan da aka samu da tsoffin kawayenta a nahiyar.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya gana da takwaransa a gidan tarihi na Invalides mai dimbin tarihi, tare da ziyarar aiki ta farko da wani shugaban Najeriya ya kai sama da shekaru ashirin.