Ma’aikatan NAHCON da hukumomin alhazai na jihohi su ne jigon tafiyar mu – Shugaban NAHCON

Shugaban NAHCON

Spread the love

Shugaban Hukumar Alhazai ta Ƙasa, NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman ya baiyana cewa ma’aikatan hukumar da kuma hukumomin alhazai na jihohi su ne jigon tafiyar hukumar.

Farfesa Usman ya baiyana hakane a ganawa da ya yi da shugabannin hukumomin alhazai na jihohi a jiya Laraba a shelkwatar hukumar da ke Abuja, a wani bangare na shirye-shiryen Hajjin baɗi.

Ya kuma jaddada ƙudurin sa na ganin hukumar ta samu nasara wajen yin aikin hajji cikin nasara ba tare da matsaloli ba.

Farfesa Usman ya kuma tabbatar wa shugabannin hukumomin alhazai na jihohi da kokarin da NAHCON ke yi na biyan su kaso su na kashi 2 cikin 100 na kuɗaɗen aiyuka da take canja duk shekara.

VANGUARD NEWS ƙarshe ya yi kira ga hukumomin da kuma masu ruwa da tsaki a fannin Hajji da su baiwa NAHCON haɗin kai don samun nasarar shirye-shiryen aikin Hajjin 2025.

Labarai Masu Alaka

Iyalan shugaban Miyetti Allah sun bukaci a sako shi, 2024


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button