Ma’aikata a Zamfara sun yi barazanar shiga yajin aiki

shiga yajin aiki

Spread the love

Ƙungiyar ƙwadago ta NLC rehen jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya ta sanar da shirin ma’aikatan jihar na shiga yajin aiki nan da ƙarshen wannan wata na Nuwamba, muddin gwamnatin jihar ba ta fara biyan sabon albashi mafi ƙaranci na naira dubu saba’in ba.

Ƙungiyar ta ce matakin jan ƙafar na nuna yadda wasu gwamnonin jihohi ba su jin tausayin ma’aikata musamman a wannan lokaci da al’umma ke fama da tsadar rayuwa inda sukace shiga yajin aiki shine yaren da gwamnatin takeji.

Gwamnatin Zamfara dai ta sanar da amincewa da naira dubu 70 ne a matsayin mafi ƙarancin albashi ga ma’aikatan jihar.

Sun kuma ce tabbas matukar gwamnati bata biya mafi karancin abashi ba zasu shiga yajin aiki.

Ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziki sun ƙaddamar da yaƙi da yunwa da talauci

Ƙungiyar ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziƙi na duniya ta G20 ta ƙaddamar da shirin yaƙi da yunwa da kuma kawar da talauci a yayin buɗe taronta na shekara-shekara karo na 19 wanda ake yi a birnin Rio de Janeiro na Brazil.

Shirin da duka ƙasashen ƙungiiyar suka sanyawa hannu za a gudanar da shi ne tsakanin shekarun 2025 zuwa 2030.

Shugaban Brazil Luiz Lula da Silva ya ce shirin wanda aka fara aiwatar da shi tun daga watan Yuli tuni na da goyon bayan sama da ƙasashe 80 a duniya, bayan ga gwamman gwamnatoci da ƙungiyoyin fararen hula.

Farashin kayayyaki sun tashi a Burtaniya saboda tsadar makamashi

Hauhawar farashin kayayyaki a Burtaniya ya ƙaru a watan da ya gabata saboda ƙaruwar kuɗin makamashi, kamar yadda alƙaluman gwamnati suka nuna.

Hauhawar farashin, ya ƙaru ne da kashi 2.3 a shekarar a watan Oktoba, wanda ƙari ne daga kashi 1.7 a watan Satumba.

Kuɗin wutar lantarki da gas da matsakaicin gida ke biya ya tashi ne zuwa £149 a watan da ya gabata, amma dai duk da haka farashin na tashi ne kaɗan-kaɗan.

Grant Fitzner, babban masanin tattalin arziki a Hukumar Ƙididdiga ta ƙasar ya ce farashin makamashin na cikin abubuwan da suke jawo tashin farashin kayayyaki a ƙasar.

“Kayayyakin da masana’antu ke buƙata sun yi tsada, kuma suna ƙara tsadar, ga kuma faɗuwar farashin ɗanyen mai,” in ji shi.

Wani mazaunin Burtaniya mai suna Darren Jones, ya ce gwamnati ta san, “iyalai na shan wahala saboda tsadar rayuwa. Muna tunanin akwai abin da ya kamata gwamnati ta yi.”

Ƴan Boko Haram sun kashe sojoji a Borno

Sojoji
Kashe sojoji

Ƴan Boko Haram sun kai hari a wani sansanin sojoji da ke Borno, inda suka kashe wasu sojoji, sannan ake tunanin sun yi awon gaba da wasu makamai.

Wata majiya ce ta tabbatar wa tashar Chahttp://Channelnnels aukuwar lamarin, inda ta ce mayaƙan Boko Haram na ɓangaren IS ne suka kai farmakin a sansanin soji da ke garin Kareto a ranar Asabar.

Majiya ta ce an kashe kusan sojoji 20, amma hedkwatar tsaro ta Najeriya ta ce sojoji biyar aka kashe mata a harin.

Sai dai majiyar ta ƙara da cewa an gwabza yaƙi sosai tsakanin ƴan Boko Haram ɗin da sojoji, sannan wani ɗan ƙunar bakin wake ya tayar da motar da yake ciki, wanda a ƙarshe ƴan Boko Haram ɗin suka ƙona motocin sojoji 14.

A nata ɓangaren, gwamnatin jihar Borno ta yi sojojin Najeriya jaje bisa rasa jami’anta a garin na Kareto.

An kama sojoji a Brazil bisa zargin yunƙurhttp://Abbapantamiin kashe shugaban ƙasa Lula a 2022

Ƴansandan Brazil sun kama mutum biyar da ake zargi da yunƙurin kashe shugaban ƙasar, Luiz Inácio Lula da Silva kafin a rantsar da shi.

Huɗu daga cikin waɗanda aka kama sojoji ne, sai wani ɗansanda, kamar yadda kafofin watsa labarai na ƙasar suka ruwaito.

Ana zarginsu ne da kitsa kashe Lula da mataimakinsa Geraldo Alckmin a ranar 15 ga Disamba bayan sun lashe zaɓen shugaban ƙasar, kimanin mako biyu kafin a rantsar da su.

Lula ya lashe zaɓe a Oktoban 2022, inda ya kayar da shugaban ƙasar mai-ci, Jair Bolsonaro, wanda bai bayyana amincewa da kayin ba.

Haka kuma mako ɗaya bayan an rantsar da Lula, magoya bayan Bolsonaro sun kutsa majalisa da Kotun Ƙolin da fadar shugaban ƙasar, suka yi ɓarna, kafin ƴansanda suka fatattake su, tare da kama wasu.

Tun lokacin ne ake binciken lamarin da ma na yunƙurin kashe Lula, amma wannan karo na farko da aka tsare waɗanda ake zargi suna da hannu.


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button