Ma’aikaciyar lafiya da ta shafe shekaru 6 a hannun ƴan Boko Haram ta shaƙi iskar ƴanci

Spread the love

Malamar jinya mai shekaru 42, Alice Loksha, da aka sace a shekarar 2018 daga hannun ‘yan Boko Haram a Jihar Borno, ta samu yancinta bayan shekaru shida.

Da yake magana da manema labarai a Maiduguri, babban birnin jihar, a ranar Juma’a, Kwamandan Rundunar Hadin Gwiwa, Operation Hadin Kai, Arewa maso Gabas, Manjo Janar Wahdi Shuaibu, ya bayyana cewa an kama ta ne yayin da take aiki a ofishin UNICEF da ke Kala Balge.

Kwamandan, wanda Mataimakinsa, Manjo Janar Kenneth Chigbu, ya wakilta, ya kuma sanar da kubutar wata mata, Fayina Ali, da aka kama a 2020 lokacin da take tafiya daga Kaduna don yin aiki kan fansar mutuwar dan uwanta.

A cewarsa, dukkansu sun yi aure da mayakan yayin da suke tsare.

“An tilasta ta auri Abu Umar, wanda suka haifi ɗa tare mai suna Mohammed.

“Bayan mutuwar Abu Umar, an tilasta ta auri wani kwamandan ISWAP mai suna Abu Simak. Daga baya ta tsere daga sansanin Dogon Chuku a ranar 24 ga Oktoba, 2024, sannan ta isa shelkwatar TC a ranar 29 ga Oktoba, 2024, inda aka ba ta kulawar lafiya.”


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button