Lagbaja: Shugaba Tinubu ya dage taron majalisar zartarwa ta tarayya

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayar da umarnin dage taron majalisar zartaswa ta tarayya har zuwa wani lokaci.

Spread the love

Cikin wata sanarwa da maitaimaki na musamman ga shugaban kasar ya fitar Bayo Onanuga ya ce an dage zaman majalisar ne domin girmama Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, babban hafsan sojin kasa, wanda ya mutu a daren ranar Talata.

Janar Lagbaja ya rike mukamin babban hafsan sojin kasa daga ranar 19 ga watan Yuni, 2023, har zuwa mutuwar sa a ranar 5 ga Nuwamba, 2024.

Shugaba Tinubu ya kuma ba da umarnin a sassauta kasar a ma’aikata na fadin kasar na tsawon kwanaki bakwai domin karrama Janar din.

A safiyar yau ne shugaba Tinubu ya jajantawa iyalan Lagbaja da rundunar sojojin Najeriya bisa mutuwar sa.

Shugaban ya kuma ya ba da gagarumar gudunmawar da lagbaja ya bayar ga al’umma.


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button