Kungiyar tuntuba ta arewa ta dakatar da shugaban ta na kasa

Kungiyar tuntuba ta Arewa ta dakatar da shugaban ta na kasa kan sukar manufofin Tinubu

Spread the love

A ranar Alhamis ne kungiyar tuntuba ta Arewa, wato Arewa Consultative Forum, ta dakatar da shugabanta, Mamman Osuman, SAN.

Kungiyar tuntuba ta arewa ta dakatar da shugaban ta na kasa
Shugaban kungiyar tuntuba ta Arewa

Punch ta ruwaito cewar Dakatar da shugaban na zuwa ne sa’o’i 24 bayan sukar manufofin gwamnatin shugaba Bola Tinubu tare da bayyana zabin ‘yan takara a zaben 2027.

Idan za ku iya tunawa cewa kungiyar tuntuba ta Arewa ta gudanar da taron ta na masu zartarwa a ranar Laraba, 20 ga watan Nuwamba, 2024, a hedikwatar ta da ke jihar Kaduna.

A wata sanarwa mai sa hannun Alhaji Bashir Muhammad da Alhaji Murtala Aliyu, ƙungiyar tuntuɓa ta musanta wasu bayanai da ke yawo cewa sun bayyana goyon bayan fito da ɗantakarar shugaban ƙasar Najeriya daga yankin arewa a 2027.
“Shugaban kungiyar ya yi wadannan kalamai ne ba tare da tuntuba ko tattaunawa da wasu shugabanni da mambobin kungiyar ta tuntuba ta Arewa ba, wanda hakan ya nuna ra’ayin Mista Osuman ne kawai.

“kungiyar tuntuba ta Arewa ta yi watsi da kalaman Mista Mamman Mike Osuman gaba daya.
A saboda haka ne shugabannin kwamitin amintattu na kungiyar tuntuba ta Arewa da na zartarwa suka yanke shawarar dakatar da Mista Mamman Mike Osuman nan take,” in ji sanarwar.

Dattawan Arewa sun bukaci sojoji su kawar da kungiyar ta’addanci ta Lakurawa.

Wadannan kalaman na zuwa ne bayan da aka samu wasu bayanai da wasu jaridun Najeriya suka wallafa da ke cin karo da juna da aka danganta da shugaban kungiyar tuntuba ta dattawan arewacin Najeriyar, Mamman Mike Osuman, da aka ce ya fadi cewa lokaci ya yi da yankin ya dace ya fito da shugaban da zai jagoranci Najeriya a shekarar 2027, da kuma ya san zafin al’ummarsa.

Kungiyar ta bayyana cewa an kafa wani kwamiti domin gudanar da bincike.

Gwamnan Kano ya miƙa yaran da gwamnatin tarayya ta saka ga iyayen su

Kungiyar tuntuba ta arewa ta dakatar da shugaban ta na kasa

Zanga-zanga: Gwamnan Kano ya miƙa yaran da gwamnatin tarayya ta saka ga iyayen su

Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya gargadi matasa 76 da ake zargi da hannu a satar kayayyaki yayin zanga-zangar EndBadGovernance da ta gabata, wadanda gwamnatin jihar ta gyara halayensu, su zama jakadu nagari kuma su rika mutunta dokokin kasa.

Daily Nigerian tace Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin mika yara 71 daga cikinsu ga iyayensu, a wani taro da aka gudanar a Asibitin Kwararru na Muhammadu Buhari da ke Kano.

Da yake jawabi ta bakin Shugaban Ma’aikatansa, Alhaji Wada Sagagi, ya yi kira ga yaran da su kasance masu bin doka kuma su guji duk wani aikin da ya sabawa doka a nan gaba.

Ya kuma bayyana cewa gwamnati za ta dauki nauyin karatun duk yaran da aka gyara, yayin da wadanda suka kammala karatunsu na NCE za a basu aikin yi a lokacin daukar ma’aikata na gaba.

A jawabin da ya yi a madadin iyayen yaran da aka gyara, Malam Nura Muhammad ya yaba wa Gwamnatin Jihar Kano bisa daukar dawainiyar yaran tun daga lokacin kama su har zuwa lokacin da aka sake su.

Tinubu ya bada umurnin a saki yaran da aka kama kan zanga-zangar tsadar rayuwa.

Tinubu ya bada umurnin a saki yaran da aka kama kan zanga-zangar tsadar rayuwa.

Majalisar Wakilai ta ki amincewa da kudirin yin wa’adi ɗaya na shekara 6 ga shugaban ƙasa da gwamnoni

Majalissar wakilai ta bukaci kamfanin raba wutar lantarki su zuba jari da yakai N500bn

Majalisar Wakilai ta kasa ta ki amincewa da karatu na biyu na kudirin da ke neman samar da wa’adin shugabancin shekaru shida kacal ga shugaban kasa da gwamnoni.

Majalisar ta yi watsi da kudirin ne yayin zamanta na ranar Alhamis.

Kudirin dai an gabatar da shi ne karkashin jagorancin dan majalisar, Ikenga Imo Ugochinyere tare da sauran mambobi 33.

An gabatar da kudirin domin karatu na biyu ne daga babbar mai daukar nauyin sa, Ugochinyere, sannan aka goyi bayan hakan.

Sai dai, yayin da Kakakin Majalisar, Abbas Tajuddeen, ya mika kudirin don kada kuri’a ta baki, muryoyi masu cewa “A’a” sun fi yawa daga mambobin majalisar.

A karshe, Kakakin ya sanar da cewa wadanda suka ce “A’a” sun yi rinjaye, wanda hakan ya nuna cewa kudirin bai samu amincewa ba kuma ya fadi a karatu na biyu.

Me ya sa kasafin kuɗin Najeriya ke dogaro da bashi?

Kungiyar tuntuba ta arewa ta dakatar da shugaban ta na kasa

Ana ci gaba da cecekuce kan bukatar da shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya mika wa majalisar dokokin ƙasar, ta amince wa ya karbo wani sabon bashi na dala biliyan biyu da miliyan dari biyu, wato kusan naira tiriliyan biyu daga waje, don samar da kudin aiwatar da wani bangare na giɓin kasafin kudin wannan shekara ta 2024.

 

Masu sukar lamarin dai suna ganin ƙaruwar bashin da kasar ke ciwowa daga waje dai wata babbar barazana ce ga gudanar da tattalin arziki yadda ya kamata.

 

Akwai damuwar da wasu ke ta bayyanawa game da yadda kasafin kudin badi shi ma zai dogara matuka kan bashi musamman kungiya masu zaman kansu.

 

Tun da bukatar karbo sabon bashin karasa aiwatar da kasafin kudin Najeriyar na bana ta taso dai, ake ta bayyana damuwa da ganin baiken abin.

 

Kodayake Dokta Murtala AbdulLahi Ƙwara, malami a sashen nazarin tattalin arziki na jami’ar Umaru Musa Ƴar-Adua da ke Katsina, yana ganin har yanzu yawan irin wannan bashi da kasar ke ciwowa daga waje, bai kai ga munana ba.

 

“Har yanzu bashin da Najeriya ke karɓa bai yi muni ba idan aka ɗora shi kan GDP, masana na ganin cewa sai bashi ya kai kashi biyu cikin uku na GDPn ƙasar ne zai zama mai ta’annati.”

 

Me ya sa ake cecekuce?

 

Buƙatar karbo rancen domin cike giɓin kasafin kuɗin Najeriyar na bana ya haifar cecekuce da saɓanin ra’ayi

 

Masanin tattalin arziki Dokta Murtala Abdullahi Kwara na ganin al’amarin bashi ga tattalin arziƙi ba gaba daya ne yake da muni ba, sai dai me aka yi da bashin shi ne abun tambaya.

 

“Yawancin kuɗin da ake ciwo wa bashi a Najeriya ana amfani da su ne wajen tafiyar da gwamnati, wadanda suke zuwa aljihun wasu mutane shafaffu da mai, wadanda suke riƙe da madafun iko,” in ji shi.

 

Masanin ya ƙara da cewa ya kamata duk bashin da za a ciwo a yi amfani da shi wajen assasa sana’a ko kuma inganta masana’antu da za su fitar da mutane daga talauci da samar wa mutane ayyukan yi.

 

Wasu masanan na ganin idan aka shiga irin halin da Najeriya ta tsinci kanta a fannin tattalin arziki, kamata ya yi gwamnati ta waiwayi cikin gida don neman mafita, a madadin ƙara ciwo bashin.

 

Sai dai fadar shugaban Najeriyar ta ce batun ba shi abu ne da ake yi kuma yana bisa tsari, kuma ‘an samu sauƙin ciwo bashi a ƙarƙashin mulkin shugaba Tinubu.

 

Malam Abdul’Azeez Abdul’Azeez, mai magana da yawun shugaban Najeriya, ya ce za a yi amfani da kudaden ne wajen tafiyar da gwamnati, musamman ayyuka, “Misali bunƙasa aikin noma, da tituna.”

 

Duk wadannan bayanai dai, har yanzu wata fargabar nan ta yi likimo, cewa bashin da Najeriyar za ta ciwo daga waje, don cike giɓin kasasfin kudin badi na iya nunka adadin wanda aka ciwo a bana.


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button