Kudirin gyaran harajin Tinubu ya ‘ba ce a hanya – Ndume
Sanata Ali Ndume ya ce kudirin sake fasalin haraji na gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu bai iso zauren majalisar ba.
Ndume ya bayyana haka ne a wata hira da gidan talabijin na Channels a ranar Talata.
Ya ce shugabannin Arewa kwata-kwata basu amincewa da kudirin ba saboda ya sabawa arewa.
Ndume ya kara da cewa ya kamata shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya gyara harkokin mulkin sa ba wai ya kara dora wa ‘yan Najeriya haraji ba.
Ya bukaci shugaban kasa da ya saurari shawarar kungiyar gwamnonin Arewa kuma ya gaggauta janye kudirin
Ndume ya ce, “Mutanenmu suna cewa ba sa son kudin harajin VAT, ba ma son jin labarinsa. Ya kamata Shugaba Tinubu ya bi shawarar kungiyar Tattalin Arzikin Kasa (NEC) da kungiyar gwamnonin Arewa ya janye kudirin nan take.
“Yan Najeriya na son biyan haraji amma sai lokacin da za su iya biya. A yanzu, mutane suna kokawa da matsin rayuwa su na neman yadda za su yi ne bawai biyan haraji ne a gabansu ba.
Ndume ya ce zai yi kyau a rufe kudirin, yana mai nuni da cewa ya fara hada kai da abokan aikin sa don kin amincewa da kudirin.
“Gwamnoni da sarakunan gargajiya sunki amincewa da kudiri, don haka, matakin da ya fi dacewa shi ne a janye shi nan take,” in ji shi.