Ku zauna a rumfunan zaɓen ku bayan kun kaɗa ƙuri’a – Makinde ya faɗa wa al’ummar Ondo
Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya bukaci al’ummar jihar Ondo da su ci gaba da zama a rumfunan zabe bayan kada kuri’a don hana duk wani “magudi”.
Makinde, shugaban jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) a yankin Kudu maso Yamma, ya yi wannan kiran a ranar Alhamis a wurin babban taron yakin neman zaben jam’iyyar a Akure, babban birnin jihar.
“Kada ku fita bayan kada kuri’a ranar Asabar. Ku tsaya a baya don tabbatar da an kirga kuri’un ku, an shigar da su cikin fom yadda ya kamata, sannan ku bi ta cibiyoyin tattara bayanai don guje wa magudi,” inji shi.
Sai dai gwamnan na Oyo ya gargadi magoya bayan jam’iyyar da su guji tayar da zaune tsaye ko cin zarafi, inda ya jaddada muhimmancin yin amfani da kuri’unsu wajen adawa da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a zabe mai zuwa.
Tun da farko, Umar Damagum, mukaddashin shugaban jam’iyyar PDP na kasa, ya bukaci al’ummar jihar Ondo da su sanya ido a ranar zabe. Ya jaddada cewa zaben zai yi matukar tasiri ga makomar kasar.
“Idan PDP ta yi nasara a ranar Asabar, za ta kawo karshen talauci da wahala a jihar,” in ji Damagum.
Ya kuma mika tutar jam’iyyar ga dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP, Agboola Ajayi.
Gwamnan jihar Bauchi kuma shugaban kungiyar gwamnonin PDP, Sanata Bala Mohammed, ya kuma yi kira ga mazauna Ondo da su zabi Ajayi ranar Asabar, yayin da jarumar fina-finan Nollywood, Rita Orji ta bukaci masu kada kuri’a da su karbi kudi daga APC kuma har yanzu su zabi PDP.
“Ya zuwa daren yau, za su fara yin kiredit a asusun ku. Ku tattara kudin, amma ku kwato jihar ku,” inji ta.
Sauran manyan baki da suka halarci gangamin sun hada da gwamnan Bayelsa Douye Diri, gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Fintiri, da gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang.
Dan takarar jam’iyyar a zaben shugaban kasa na 2023, Atiku Abubakar, bai halarci taron ba. Sai dai a baya tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi kaca-kaca da Ajayi a wata sanarwa da ofishin yada labaran sa ya fitar.