Kotun Koli ta yi watsi da karar kalubalantar dokar kafa EFCC
Kotun Koli ta yi watsi da karar da wasu Antoni Janar na jihohi suka shigar, suna kalubalantar dokar da ta kafa Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC).
Karar, wadda Antoni Janar na jihohi 16 suka fara shigar, ta nemi a rusa hukumar yaki da cin hanci da rashawa. Duk da haka, wasu jihohi sun janye daga karar, yayin da wasu suka nemi a shiga cikin karar a matsayin masu kara.
Jihohin da suka fara shigar da karar sun hada da Ondo, Edo, Oyo, Ogun, Nasarawa, Kebbi, Katsina, Sokoto, Jigawa, Enugu, Benue, Anambra, Filato, Cross-River, da Neja.
Sai dai, yayin ci gaba da sauraron karar a ranar 22 ga Oktoba, jihohin Imo, Bauchi, da Osun sun shiga cikin karar a matsayin masu kara, yayin da jihohin Anambra, Ebonyi, da Adamawa suka sanar da kudurinsu na janye karar su.
Hukumar Shari’a ta Ƙasa (NJC) ta dakatar da Mai Shari’a G. C. Aguma na Babbar Kotun Jihar Rivers da Mai Shari’a A. O. Nwabunike na Babbar Kotun Jihar Anambra daga gudanar da ayyukan shari’a.
An dakatar da su tsawon shekara guda ba tare da albashi ba, sannan za a sanya su a jerin wanda za a sanya ido a kansu na tsawon shekaru biyu bayan haka.
An yanke wannan hukuncin ne a taro na 107 na NJC wanda Babbar Mai Shari’a ta Najeriya, Kudirat Kekere-Ekun, ta jagoranta a ranakun 13 da 14 ga Nuwamba 2024.
Jimillar Alkalai guda biyar da ke kan aiki sun samu hukunci saboda aikata laifuka daban-daban na rashin da’a.
Hukumar ta kuma bada shawarar a tilasta wa wasu shugabannin kotuna biyu yin murabus saboda canza shekarun haihuwa.
An kai maroƙi kotu bisa zargin sace wayoyin abokan ango a wajen daurin aure
Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta gurfanar da wani mutum mai suna Bashir Abubakar Brigade a gaban wata kotun shari’ar Musulunci da ke zamanta a Fagge ‘Yan Alluna bisa zargin laifin satar wayoyin abokan ango a yayin daurin aure.
Daily Trust ta rawaito cewa an kama Bashir ne bisa zargin satar wayoyin hannu guda biyu da kudinsu ya kai Naira dubu 125 da kuma Naira dubu 25.
Lauyan masu shigar da kara na Jiha, Barr. Zaharaddeen Mustapha, ya karanta wa wanda ake zargin laifukan da suka hada da hada baki da kuma sata.
Sai dai ya musanta zargin da ake masa, inda ya jaddada cewa shi ba barawo ba ne, maroƙi ne kawai.
Daga bisani kotu ta bada belinsa da sharadin ya kawo dan uwansa na jini da kuma takardar shaidar wani gida da ya mallaka.
Alkalin kotun, Khadi Umar Lawan Abubakar ya dage sauraron karar har zuwa ranar 25 ga watan Nuwamba domin bayar da shaida.
2 Comments