Rundunar sojin Najeriya ta tura dakarun korar Lakurawa daga Sokoto da Kebbi 2024
Babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya buƙaci sojojin Najeriya su fatattaki Lakurawa daga jihohin Sokoto da Kebbi da ke arewacin ƙasar.
Babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya buƙaci sojojin Najeriya su fatattaki Lakurawa daga jihohin Sokoto da Kebbi da ke arewacin ƙasar.
Wata sanarwa ta ce babban hafsan ya bayyana haka ne a cikin saƙon da ya aike wa runduna ta musamman da ya tura domin aikin fatattakar Lakurawa mai suna “Chase Lakuwaras Out”. Kamar yadda BBC ta rawaito.
Da yake jawabi a madadin babban hafsan, babban kwamandan runduna ta 8 ta sojin ƙasa na Najeriya, Birgediya Janar Oluyinka Soyele, ya buƙaci sojojin su tabbatar sun kawo ƙarshen ƴan ƙungiyar Lakurawa.
Sai dai ya buƙaci sojojin su kiyaye rayuka da dukiyar al’umma na waɗanda babu ruwansu.
A cewarsa: “An zaɓi sojojin ne sannan aka horar da su, don haka ƴan Najeriya suna fata za su fatattaki Lakurawan nan baki ɗaya,” kamar yadda rahoton kamfanin dillancin labarai na Najeriya, NAN ya nuna.
Mr Soyele ya ce tun kafin aika sojojin na musamman, dakarun rundunar sun kutsa dazukan Sokoto da Kebbi, inda suka gwabza da ƴanbindigar, inda suka ƙwato bindigu da alburusai da dama.
Lakurawa, Lakurawa, Lakurawa, Lakurawa, Lakurawa, Lakurawa, Lakurawa, Lakurawa, Lakurawa, Lakurawa Lakurawa, Lakurawa.
Shettima ya tashi daga Abuja zuwa Dubai domin kaddamar da kamfanin man fetur
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya bar Abuja zuwa birnin Dubai na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa, domin wakilcin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a wajen kaddamar da kaddamar da wani kamfanin samar da man fetur da kuma ajiyar dala miliyan 315.
Ginin, cikakken kamfanin mai da iskar gas mallakin Najeriya daga Oriental Energy Limited, an shirya fara aiki a ranar 14 ga Disamba, 2024.
Stanley Nkwocha, babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai da sadarwa na ofishin mataimakin shugaban kasar, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce mataimakin shugaban kasar zai zarce daga Dubai, zuwa kasar Saudiyya inda zai gudanar da aikin Hajjin bana (Umrah) a garuruwa masu tsarki. Madina da Makkah daga 16 zuwa 19 ga Disamba, 2024.
Wani bangare na sanarwar ya ce, “A ranar 20 ga watan Disamba, mataimakin shugaban kasa Shettima zai gana da shugaban bankin ci gaban Musulunci (IsDB) a Jeddah.
Tattaunawar za ta mayar da hankali ne kan tsare-tsare na hada-hadar kudade na yankunan sarrafa masana’antu na musamman (SAPZ Phase II) da kuma inganta ayyukan IsDB a Najeriya, da nufin karfafa ayyukan noma da tattalin arzikin kasa.
Ana sa ran mataimakin shugaban kasar zai dawo Najeriya a ko kuma kafin ranar 21 ga Disamba, 2024.”
A halin da ake ciki, mataimakin shugaban kasar ya halarci daurin auren Fatiha dan karamin ministan kasafi da tsare-tsare na tattalin arziki, Sanata Abubakar Atiku Bagudu, a masallacin Sultan Bello da ke Kaduna a safiyar ranar Juma’a.
An daura auren ne tsakanin Ibrahim A. Bagudu da amaryarsa Amina Tatari Ali.
Da isar mataimakin shugaban kasar ya samu tarba daga gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani a filin jirgin sama.
Kafin daurin auren, Shettima ya yi Sallar Juma’a a masallacin Sultan Bello.
Ya samu rakiyar gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule; Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum; da kuma mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan ayyuka (Ofishin mataimakin shugaban kasa), Aliyu Modibbo Umar.
Sauran manyan baki da suka halarci daurin auren sun hada da shugaban rukunin Dangote, Aliko Dangote, gwamnan jihar Ogun, Prince Dapo Abiodun; Gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi; Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Yahaya; Gwamnan jihar Kebbi, Dr. Nasir Idris; da gwamnan jihar Sokoto, Dr. Ahmad Aliyu.
Haka kuma akwai: Sanata mai wakiltar mazabar Zamfara ta yamma, Alhaji Abdul Aziz Yari; Sanata mai wakiltar Filato ta Kudu ta Filato, Simon Bako Lalong; Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris; Ministan Kudi kuma Ministan Tattalin Arziki, Wale Edun da Karamin Ministan Tsaro, Dokta Bello Matawalle da sauran manyan baki.
Babu ruwanmu da abin da ke faruwa a Syria – Trump
Lokacin da Donald Trump tare da sauran shugabannin ƙasashen duniya suka je birnin Paris a makon da ya gabata domin ganin yadda aka sake buɗe ginin coci mai tarihi na Notre Dame Cathedral, ƴan tawayen Syria na kan hanyarsu ta zuwa Damascus domin karɓe mulki daga hannun shugaba Bashar al-Assad.
A wannan lokaci hankalin shugabanni, ciki har da Trump na bibiyar abubuwan da ke faruwa a ƙasar ta Syria.
Ya wallafa a shafinsa na sada zumunta cewa: “Syria ta zama shirme, amma ba abokanmu ba ne.”
Ya ƙara da cewa “BAI KAMATA AMURKA TA YI WANI ABU A KAI BA. WANNAN BA FAƊANMU BA NE. A BAR SU SU YI KAYANSU. KADA A TSOMA BAKI!”
Waɗannan abubuwa da zaɓaɓɓen shugaban na Amurka ya wallafa tamkar tunatarwa ce game da ƙudurinsa na tsame hannu daga cikin al’amuran ƙasashen ƙetare.
Sai dai hakan ya kuma jefa ayar tambaya kan irin abubuwan da za su faru a gaba. Ganin yadda yaƙin na Syria ya shafi yankuna da dama na duniya da hannun da shugabannin ƙasashen duniya da dama a ciki, zai iya yiwuwa a ce Trump ya ce “babu ruwan shi” da Syria a wannan lokaci da aka kawar da gwamnatin Bashar al-Assad?
Ko Trump zai janye sojojin Amurka daga ƙasar?
Shin manufofin Trump sun yi hannun-riga da na shugaban Biden ne, kuma idan haka ne mene ne amfanin duk wani mataki mai muhimmanci da Biden zai ɗauka daga nan zuwa ƴan makonnin da suka rage kafin Trump ya kama mulki?
Gwamantin Amurka mai ci a yanzu na ta karakaina kan wasu jerin tattaunawa na diflomasiyya bayan abin da ya faru na rushewar gwamnatin Assad da kuma karɓe ikon da ƙungiyar HTS ta yi – ƙungiyar da Amurka ta ayyana a matsayin ta ƴan ta’adda.
Yanzu haka sakataren harkokin waje na Amurka, Antony Blinken na zirga-zirga tsakanin ƙasashen Jordan da Turkiyya domin ganin cewa ƙasashen Larabawa da kuma na Musulmi sun goyi bayan wasu sharuɗɗa da Amurka ke son kafawa game da makomar Syria.
Amurka ta ce dole ne Syria ta riƙa bayani kan duk matakan da take ɗauka kuma kada ta zama “sansanin ta’addanci”, kada ta yi barazana ga maƙwaftanta sannan kuma dole ne ƙasar ta lalata duk wasu makaman sinadarai masu guba da take da su.
Amma a ra’ayin Mike Waltz, mutumin da Donald Trump ya zaɓa a matsayin mai ba shi shawara kan tsaro, wanda ba a riga an tabbatar masa da muƙamin ba, yana dogaro ne da wani abu guda ɗaya idan aka zo maganar alaƙar Amurka da sauran ƙasashen duniya.
A wata tattaunawa da kafar talabijin ta Fox News cikin wannan mako, Waltz ya ce “an zaɓi Donald Trump da gagarumin rinjaye ne bisa alƙawarin cewa Amurka ba ta cusa kanta cikin ƙarin wasu yaƙe-yaƙe a Gabas ta tsakiya ba.”
Ya ce abubuwan kawai da Amurka ke da “ra’ayi sosai a kai” su ne ƙungiyar IS da kuma “ƙawayenmu na yankin Gulf”.
Bayanan Waltz tamkar bayani ne a taƙaice kan ra’ayin Trump game da Syria, wadda wani ɓangare ne na turakun rikice-rikicen da ake fama da su a Gabas ta tsakiya.
One Comment