Ko yaƙin da Taliban ke yi da sauyin yanayi alheri ne ga maƙwabtansu? 2024
Yana da Faɗin sama da mita 100 kuma ya miƙe har iya ganin ido, katafaren aikin gine-gine da ƴan Taliban ke gudanarwa a arewacin Afganistan wani babban abin gani ne.
Yana da Faɗin sama da mita 100 kuma ya miƙe har iya ganin ido, katafaren aikin gine-gine da ƴan Taliban ke gudanarwa a arewacin Afganistan wani babban abin gani ne.
Wani ɓangare na manufarsa shi ne yin wani abu da ba a saba danganta shi da ƙungiyar da ta karɓi mulki a shekarar 2021 – yaƙi da sauyin yanayi. A wani rahoto da BBC Hausa ta fitar tace.
An kashe sama da dala miliyan 600 kuma zai kai tsawon kilomita 285 idan an kammala shi, babban magudanar ruwa ta Qosh Tepa za ta kawo ruwan da ake matuƙar buƙata zuwa larduna uku a arewacin Afghanistan.
Wannan gagarumin aikain ba magance sauyin yanayi kaɗai zai yi a yankunan noma da ake da su ba, har ma da nufin mayar da busasshiyar ƙasa mai fadin murabba’in kilomita 5,000 zuwa ƙasa mai albarkar noma.
Taliban na fatan za ta inganta yanayin abinci da kuma rayuwar dubban ɗaruruwan mutane.
Damuwar ƙungiyar game da sauyin yanayi ya ɗauki hankulan duniya a farkon wannan makon lokacin da wakilai da dama suka isa taron sauyin yanayi na COP29 a Azerbaijan. Taliban
Yayin da akasarin ƙasashen duniya suka yi watsi da su, an bai wa ƴan Taliban damar halartar taron saboda munanan matsalolin da Afganistan ke fuskanta. Taliban
An lissafa ƙasar a matsayin ɗaya daga cikin goma da ke cikin haɗari kuma mafi ƙarancin shiri don tunkarar matasalar sauyin yanayi.
A wajen taron, ƙungiyar Taliban ta buƙaci ƙasashen duniya da suka dakatar da bayar da kuɗaɗe don ayyukan daƙile sauyin yanayi a lokacin da ƙungiyar ta karɓe mulki, da dawo da shirin ba su gudummawa.
Matuil Haq Khalis, shugaban hukumar kare muhalli ta Afganistan, ya shaidawa manema labarai cewa, “Muna fatan a ƙarshen wannan taro, za a samar da mafita ga ayyukan da aka dakatar a Afghanistan.” Taliban
Canal Qosh Tepa yana ɗaya daga cikin ƴan ayyukan da ke da alaƙa da yanayi da ke ci gaba da gudana.
Gwamnatin Taliban ce ta samar da kuɗaɗen ta kuma fara gudanar da aiki ta ba tare da wani taimako daga waje ba kuma tana samun ci gaba cikin sauri inda ta riga ta gina sama da kilomita 100.
Babban aikin kuɗi ne ga ƙasar da ta ga tattalin arzikinta ya ragu da sama da kashi 2 cikin 100 tun lokacin da ƙungiyar ta karɓi ragamar mulki kuma inda sama da kashi 90 cikin ɗari na mutanen ƙasar ke rayuwa cikin talauci. Taliban
An fara tsara shirin ne a cikin shekarun 1970s, tare da manufar daƙile bushewar arewacin Afghanistan. An dakatar da aikin na shekaru da dama, galibi saboda da rikice-rikicen da aka daɗe ana fama da su a ƙasar. Taliban
Gwamnatin da ta gabata ta ɗora alhakin tafiyar hawainiya da aikin ke yi kan ayyukan da tsagerunTaliban ke yi a yankin da .
Barazanar da ake fuskanta daga sauyin yanayi ya sanya ana buƙatar magudanar ruwan cikin gaggawa.
Haji Rajab na ɗaya daga cikin masu buƙatar wannan taimakon.
Ya yi noma a kusa da magudanar ruwan a gundumar Aqcha, a lardin Jawzijan, tsawon rayuwarsa, amma ruwan bazara da ya dogara da shi ya ci gaba da raguwa.
Da yake nome busasshiyar ƙasa a ɗaya daga cikin gonakinsa, manomin mai shekaru 70 ya ce yankin ya yi fama da fari na shekaru uku kuma babu amfanin gona a nan.
“Mutane suna kokawa. Ba su da isassun kuɗaɗe kuma fari ya sanya su cikin matuƙar wahala,” inji shi.
A cikin ƙasar da sama da kashi 80% na al’ummar ƙasar suka dogara kan aikin noma babbar matsala ce – sama da mutane miliyan 12 suna fama da matsanancin ƙarancin abinci.
Sai dai ba Afganistan ba ce kaɗai a yankin da ke fama da matsalar sauyin yanayi ba kRuwan zai samu ne daga kogin Amu wanda ya ratsa kan iyakar arewacin Afganistan ya wuce zuwa Uzbekistan da Turkmenistan. Taliban
Babbar cibiyar nazarin harkokin tsaro ta Manohar Parrikar, ta yi gargadin lokacin da magudanar ruwa ta fara aiki sosai, za ta iya rage yawan ruwan da ke kai wa ƙasashen makwabta da kashi daya cikin biyar. Taliban
Kasancewar Turkmenistan da Uzbekistan sun dogara sosai kan kogin Amu don aikin noma, sun nuna damuwa kan aikin magudanar ruwan.
Wani rahoto da cibiyar ta fitar ya ce: “lamarin na ci gaba da ta’azzara sosai yayin da ƙasashen ke fuskantar rashin tabbas.”
An kuma nuna damuwa kan saurin da ake yi wurin aiwatar da aikin da kuma ko akwai isassun kwararru a Afganistan don kammala irin wannan gagarumin aikin ba tare da taimako daga waje ba. Taliban
Ƙungiya mai rajin kare muhalli ta ‘Rivers Without Borders’ ta bayar da rahoton cewa, tuni aka samu wani babban malalar ruwa daga magudanar a cewar binciken da suka yi na hotunan tauraron ɗan adam.
Jami’ai a Afganistan dai sun ce wannan gagarumin aikin yana tafiya yadda ya kamata kuma za a kammala shi a kan lokaci a shekarar 2028. Taliban
Zabihullah Miri shi ne babban injiniya kuma a baya ya yi aikin haɗin gwiwa da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa da dama kan manyan ayyukan gine-gine na farar hula a ƙasar.
Ya yi imanin cewa damuwa da ake nunawa game da ruwan da magudanar za ta karkatar daga kogin Amu bai dace ba.
“Za mu iya cewa ba wani babban lamari ba ne kuma ba zai shafi ruwan da wasu yankuna ke samu ba,” in ji shi.
Mutane da dama a Afghanistan suna fatan hakan ne lamarin zai kasance.
Iyalan Abdul Mobin sun kwashe shekaru da dama suna noma gona ɗaya a gundumar Dawalatbad, a lardin Balkh.
Amma a cikin shekaru uku da suka gabata babu abin da aka iya shukawa saboda fari.
Duk da cewa ba a kammala aikin magudanar ruwan ba, ruwan da ke cikin kasa da ke ɓulɓula a cikinsa ya shayar da gonarsa har ya sake fara noma.
Ga manomin mai shekaru 37, wanda ke tallafa wa matarsa da ƴaƴansa uku da surukarsa, wannan lamari ne da zai yi matuƙara sauya rayuwarsa. Taliban
“Ina so in gina gida don iyalina, ina so in dawo nan da zama,” in ji shi. “Saboda za mu sami ruwa kuma za mu yi noma mu kuma shuka duk abin da muke buƙata a wannan ƙasa, tun daga tumatir zuwa ƴaƴan itatuwa.”
Yayin da barazanar sauyin yanayi ke ci gaba da ƙamari, ba ƙaramin fata ake da shi kan wannan katafaren aikin ba.
An fara taron majalisar dinkin Duniya kan sauyin yanayi na COP29
A ranar litinin ne aka buɗe taron Majalisar Ɗinkin Duniya kan sauyin yanayi na COP29 a Azerbaijan, wanda ke matsayin irinsa na farko da zai gudana bayan nasarar Donald Trump a zaɓen Amurka, cike da fargabar yiwuwar ya janye ƙasar shi daga ƙoƙarin da ake na yaƙi da ɗumamar yanayi.
Fiye da wakilcin ƙasashe 70 da ƙungiyoyi baya ga ƴan fafutukar yaƙi da matsalar ɗumamar yanayi ne yanzu haka suka hallara a birnin Baku fadar gwamnatin Azerbaijan don halartar taron na COP29 wanda ya faro a yau Litinin ake kuma fatan kammala shi ranar 22 ga watan nan.
Ana saran taron ya mayar da hankali kan barazanar da ke tunƙaro duniya bayan hasashen masana da ke gargaɗin cewa ana tunƙarar wani yanayi da ka iya zama mafi ƙololuwar zafin da duniya za ta fuskanta.
Tuni dai zaɓaɓɓen shugaban na Amurka Donald Trump ya sha alwashin fitar da ƙasar ta shi daga yarjejeniyar yanayi ta birnin Paris wadda ke da nufin rage tiriri mai guba da ke haddasa ɗumamar yanayi daga ƙasashe masu manyan masana’antu.
Mene ne COP29?
Ana kiran taron Majalisar Dinkin Duniya na shekara-shekara kan sauyin yanayi, ”Conference of Parties”, ko COP kuma a takaice.
A wannan shekara za a gudanar da shi karo na ashirin da tara, wanda aka fara a birnin Berlin a shekarar 1995. Manufar taron na COP shi ne takaita fitar da iskar Carbon Dioxide (CO2) da kuma daƙile dumamar yanayi zuwa ma’aunin Celsius 1.5, matakin da a ke kafin bunƙasar masana’antu.
Wani muhimmin batu da za a tattauna a wannan shekara shi ne tara kuɗaɗe ga ƙasashe masu tasowa domin su iya tunkarar matsalar ɗumamar yanayi. Ƙasashe da dama sun riga sun fuskanci yanayi maras tabbas da gurɓacewar iska. Amma ƙasashe masu ƙaramin ƙarfi na fuskanytar ƙalubale sauyi zuwa amfani da makamashi mai tsafta.
A shekara ta 2009, yayin da ake gudanar da COP15 a Copenhagen, an amince da cewa za a ware dala biliyan 100 a duk shekara daga ƙasashen da suka ci gaba don tallafaw ƙasashe masu tasowa su tunkari sauyin yanayi.
A shekarar 2015, an tabbatar da wannan adadin kuɗaɗen da za a yi aiki da shi daga 2020 zuwa 2025. A cewar rahotanni daga ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa, an cimma burin tara dalar Amurka biliyan 100 a karon farko a shekarar 2022.
Bayan 2025, wani shiri na daban, mai taken “New Collective Quantitative Target on Climate Finance” (NCQG) zai fara aiki. Burin tara waɗannan kuɗa ɗe yana ɗaya daga cikin manyan batutuwa da za a tattauna a COP29 a Baku wannan watan.
Ƙasashe masu tasowa sun ce suna buƙatar kuɗaɗen da suka kai tsakanin dala tiriliyan 1.1 zuwa dala tiriliyan 1.3, amma ƙasashen da suka ci gaba suna son a bar wannan adadin a dala biliyan 100.