Kirsimeti: An fara zirga zirga na jirgin kasa kyauta ga ƴan Najeriya a duk faɗin ƙasar na 2024

An fara zirga zirga na jirgin kasa kyauta ga ƴan Najeriya a duk faɗin ƙasar 

Spread the love

A ranar Juma’a ne gwamnatin tarayya ta fara zirga-zirgar jiragen kasa kyauta a fadin kasar domin saukaka tsadar sufurin fasinjoji a fadin kasar a lokacin bikin Kirsimeti.

An fara zirga-zirga Kirsimeti
Jirgin kasan Nijeriya

Mukaddashin Manajan Daraktan Hukumar jiragen kasa ta Najeriya, Ben Iloanusi ya bayyana haka a lokacin da yake maraba da rukunin farko na fasinjojin da suka isa tashar jirgin kasa ta Kubwa da ke Abuja daga Rigasa.

Sai dai ya ce hukumar na daukar matakan magance matsalolin tsaro da ake tunanin fasinjojin za su iya fuskanta a yayin bikin Kirsimeti da sabuwar shekara.

Da yake karin haske, ya bayyana cewa “za’a gudanar da tafiye-tafiyen kyauta ne wanda jirgin zai dauki fasinjoji 20,000 a kullum saboda ita gwamnatin tarayya ta yi kiyasin zata ɗauki fasinjoji 340,000 ne kafin hidimar Kirsimeti ya kare a makon farko na watan Janairun 2025.

Ya kara da cewa tafiyar za ta kasance ne a wurare biyar da suka hada da: Abuja-Kaduna, Lagos-Ibadan, Warri-Itakpe, Portharcourt/Aba da kuma Legas Mass Transit. Daily trust 

Da aka tambaye shi abin da hukumar ke yi don magance masu yin kutse wa shirin, sai ya ce, “Tashar ta himmatu wajen samar da matakai domin hana mutane siyan tikiti da yawa.

Labarai masu alaƙa 

Shugaban nin arewa ne suka talauta yankin 

Hukumar Civil Defence ta tura ma’aikata 28,000 a fadin Najeriya don bukukuwan karshen shekara.

Kirsimeti: An fara zirga zirga na jirgin kasa kyauta ga ƴan Najeriya a duk faɗin ƙasar na 2024
Hukumar tsaron farin kaya

Babban kwamandan hukumar tsaro ta farin kaya ta Najeriya (NSCDC), Dakta Ahmed Abubakar Audi, ya bayar da umarnin a gaggauta tura jami’ai 28,300 domin samar da isasshen tsaro da kare rayuka da kadarorin kasa da kayayyakin more rayuwa a fadin jihohin tarayyar kasar nan a lokacin bikin Kirsimeti da sabuwar shekara.

Kakakin rundunar, Afolabi Babawale ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Juma’a.

Dokta Audi, ya bukaci dukkan kwamandojin Shiyya da na Jihohi da su tashi tsaye ta re da nuna kwarewar su ta leken asiri, domin magance duk wani abi dazai jawo koma baya a bikin Kirsimeti da sabuwar shekara.

Hukumar za ta ci gaba da kasancewa kan gaba wajen kare kadarorin kasa da ababen more rayuwa a fadin kasar nan, wanda shi ne hurumin hukumar da doka ta bata dama.

Yakara da cewa, masu ra’ayin aikata laifuka kan yi amfani da lokacin bukukuwa don aiwatar da munanan ayyukansu.

Don haka yake bada shawari ga al’umma da su kasance a masu kula da harkokin da suke na yau da kullum a yayin bikin Kirsimeti da sabuwar shekara, in ji shi.

Hukumar ta kara da cewa an zabo jami’ai da aka tura ne daga dukkan jami’an tsaro, dakaru na musamman, da jami’an leken asiri, da yaki da muggan ayyuka.

Ya kara da cewa, za a sanya ido sosai kan duk wuraren da ake bukukuwa da suka hada da wuraren shakatawa, tarukan addini, wuraren fakin na motoci, wuraren kasuwanci da sauran muhimman wurare..


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button