Kashim zai mika yaran da aka kama ga Gwamnonin jihohinsu
A yau Talata ake sa ran Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima zai miƙa yaran nan da aka gurfanar bisa zargin shiga zanga-zanga ga gwamnonin jahohin su.
Shettima zai Mikawa Gwamnoni kananan yaran da aka tsare bisa shiga Zanga-zangar yunwa.
Majiyoyi sun bayyana cewa taron, wanda za a gudanar a Babbar Kotun Tarayya, zai kunshi bikin mikawa gwamnonin yaran a hukumance, inda kowanne gwamna zai karɓi yaro domin kula da su da kuma sake mayar da su cikin al’umma.
Wannan mataki ya biyo bayan suka daga ciki da wajen ƙasa dangane da halin da yaran suka tsinci kansu a karkashin mulkin Shugaba Tinubu.