Gwamnatin Adamawa ta dauki matakin kawo karshen rikicin manoma da makiyaya 2024

Gwamnatin jihar Adamawa ta dauki wani muhimmin mataki na kawo karshen rikicin manoma da makiyaya a jihar.

Spread the love

Gwamnatin jihar Adamawa ta dauki wani muhimmin mataki na kawo karshen rikicin manoma da makiyaya a jihar.

Gwamnatin Adamawa ta dauki matakin kawo karshen rikicin manoma da makiyaya
Umaru Fintiri

A cewar sakataren gwamnatin jihar Auwal Tukur, gwamnatin ta yanke shawarar ganowa tare da samar da wuraren kiwo domin rage takun saka tsakanin kungiyoyin biyu. Manoma

Daily trust ta rawaito cewa, An cimma wannan matsaya ne bayan wani gagarumin taron tsaro da Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya jagoranta, wanda ya hada hakimai da sarakunan gargajiya da shugabannin kansiloli.

Taron dai ya mayar da hankali ne kan magance tashe tashen hankula musamman a lokacin girbi. Manoma

Domin magance musabbabin rikice-rikicen, gwamnati ta yi shirin shirya tarukan karawa juna sani da taron karawa juna sani ga sarakunan gargajiya, tare da sanin rawar da suke takawa a cikin al’umma. Manoma

Wannan yunkuri na da nufin ilmantar da su a kan nauyin da ke kansu da kuma karfafa su don taimakawa wajen magance matsalolin tun da wuri. Manoma

Gwamnatin ta kuma bayyana makiyayan da ke kan iyaka a matsayin babban bangaren matsalar tare da shirin tantancewa da kuma yi wa duk makiyayan da ke kiwo a jihar rajista. Manoma

An yi kira ga al’umma da su taimaka wa gwamnati a kan wannan yunkurin, inda aka umurci shugabannin gargajiya da su fara taro don magance matsalolin da ke faruwa a kananan hukumominsu.

Bugu da kari, gwamnati ta himmatu wajen kara zuba jari a harkar noma, da yin amfani da fasahohin zamani don bunkasa abinci da kiwo.

Isra’ila ta kai hare-hare ‘sama da 300’ a Syria bayan kifar da gwamnatin Assad

Isra'ila ta kai hare-hare 'sama da 300' a Syria bayan kifar da gwamnatin Assad
Hare hare

Rahotanni sun nuna cewa jiragen sama na Isra’ila sun kai ɗaruruwan hare-hare ta sama a Syria, ciki har da Damascus babbn birnin ƙasar.

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan’adam ta Syrian Observatory for Human Rights (SOHR) mai mazauni a Birtaniya ta tattara sama da hare-hare 310, waɗanda dakarun IDF suka kai tun bayan kifar da gwamnatin Assad a ranar Lahadi.

Hare-haren sun mayar da hankali ne kan kadarorin sojin Syria, ciki har da ma’ajiyar makamansu da filin jirgin sama da cibiyoyin bincike.

Isra’ila ta ce tana kai hare-haren ne domin hana makamai faɗawa “hannun masu tsattsauran ra’ayi” a Syria.

Ƙungiyar SOHR ta ce hare-haren sun fi ƙamari a Aleppo da Damasucs da Hama, kuma ko a daren Litinin kaɗai an kai sama da hare-hare 60.

Rahotannin sun ce an lalata duk wuraren da aka kai hare-haren.

BBC ta tantance bidiyon wasu daga cikin hare-haren, daga cikinsu kuma ciki har da wani wanda aka kai a sansanin sojin ruwa da ke Latakia.

Rami Abdul Rahman, shi ne shugaban SOHR kuma ya kwatanta hare-haren da yunƙurin “kassara sojin Syria”.

IDF ta ƙaryata labarin, inda ta shaida wa BBC cewa labarin hare-harenta a Damascus “ƙarya ne.”

A ranar Litinin, rundunar sojin Isra’ila ta saki waso hotunan lokacin da sojojinta suke tsallake tuddan golan da ta mamaye domin shiga Syria ta yankin raba-grdama da dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniye suke aiki.

Ƙwace iko da Isra’ila ta yi ɓangaren Syria na yankin, “wani yunƙuri ne na wucin gadi har zuwa lokacin da za a samu tsari mai kyau,” in ji firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu.

“Idan muka tabbatar da aminci daga maƙwabtanmu musamman shugabannin Syria na yanzu, za mu yi farin ciki. Amma idan ba mu samu ba, za mu yi duk abin da za mu iya domin kare Isra’il,” in ji shi a ranar Litinin.

Ma’aikatar harkokin wajen Turkiyya ta soki hare-haren na Isra’ila a yankin, inda ta zargi Isra’ila da yunƙurin “mamaye a lokaci mai muhimmanci da ake gani za a samar da tabbataccen zaman lafiya ga mutanen Syria suke nema na tsawon shekaru.”

Yankin raba-gardamar, na cikin yarjejeniyar tsagaita wuta da aka yi tsakanin Isra’ila da Syria shekarar 1974 domin raba tsakanin dakarun Syria da Isra’ila bayan da farko Isra’ila ta ƙwace iko da tuddan golan.

Amma sai Isra’ila ta mayar da golan ƙasarta a shekarar 1981, amma ƙasashen duniya ba su amince da matakin ba, duk da cewa Amurka ta amince a shekarar 2019.

Da aka tambaye shi ko IDF ta kai hare-hare a daren Litinin, ministan harkokin wajen Isra’ila Gideon Saar ya ce Isra’ila ta fi damuwa ne kan kare ƴanƙasarta.

“Shi ya sa muka kai hari a wurare masu muhimmanci, kamar misali sauran wuraren da aka haɗa makaman sinadari da makamai masu linzami masu cin dogon zango da rokoki domin gudun kar su faɗa hannun masu tsautsauran ra’ayi,” in ji shi.

A ranar Litinin, kwamitin sa ido kan makaman sinadarai ya gargaɗi Syria kan tabbatar da cewa cibiyoyin haɗa makaman na sinadarai ba a taɓa su ba.

Hare-haren Isra’ila sun zo ne bayan ƴantawayen Syria sun ƙwace babban birnin Syria, Damascus, sannan sun kifar da gwamnatin Bashar al-Assad a ƙarshen mako, inda shi da mahaifinsa suka mulki ƙasar tun shekarar 1971.

Mayaƙa ƙarƙashin jagorancin ƙungiyar Hayat Tahrir al-Sham (HTS) ne suka kutsa Damascus a ranar Lahadi, kafin daga bisani suka bayyana a talabijin na ƙasar, inda suka sanar da cewa sun ƙwace mulkin ƙasar.


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button