Kano: Likitoci a jahar Kano sun dakatar da yajin aikin bayan ganawa da Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Kungiyar likitocin Najeriya NMA ta dakatar da yajin aikin da take yi tare da maido da cikakken aikin asibitin kwararru na Murtala Muhammad da ke Kano.
Wannan ci gaban ya biyo bayan tsoma bakin gwamna Abba Kabir Yusuf ne da ya gana da shugabannin kungiyar a ranar Alhamis.
Shugaban kungiyar, Dr Abdulrahman Ali, ya tabbatar wa Aminiya faruwar lamarin.
Hakazalika, a cewar mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, matakin dakatar da yajin aikin ya zo ne bayan wata ganawa da gwamna Yusuf, inda aka sasanta rikicin da ya taso daga rashin fahimtar juna tsakanin wani likitan asibiti da kwamishina.
Dr. Abdurrahman ya nuna jin dadinsa ga matakin gaggawar da gwamnan ya dauka, wanda ya dakile ci gaba da kawo cikas ga muhimman ayyukan kiwon lafiya.
Ya kuma yi kira ga al’ummar Kano da su mika duk wani koke-koke ta hanyar hukumomin da suka dace, yana mai ba su tabbacin cewa duk wata takaddama tsakanin majinyata da ma’aikatan lafiya.