Kakakin majalisar wakilai na goyan bayan sake fasalin bangaren wutar lantarki.
Kakakin Majalisar Wakilai, Hon. Tajudeen Abbas ya yi alkawarin bayar da goyon baya ga Majalisar Dokoki ta kasa kan sauye-sauyen da ake yi a fannin samar da wutar lantarki a Najeriya, ya kuma yi kira da a hada kai da duk masu ruwa da tsaki domin inganta amincin tashar wutar lantarki ta kasa.
Dokta Abbas wanda ya bayyana haka a wajen bude taron baje kolin Injiniyan Wutar Lantarki na kasa da kasa da aka gudanar a Abuja, ya yi kira da a hada makamashin da ake sabuntawa a cikin hadakar makamashin kasar domin inganta ta yadda ya kamata.
Taron an mai take da Samar Sashin Wutar Lantarki Mai Inganci na Karni na 21: Matsayin Dokokin Ayyukan Ƙwararru”.
Kakakin majalisar wanda ya samu wakilcin mataimakin shugaban kwamitin samar da wutar lantarki na majalisar wakilai, August Gana, shugaban majalisar ya bayyana cewa a cikin shekaru da dama, an gudanar da gyare-gyare a fannin da kuma mayar da hannun jari da nufin samar da tsayayyar wuta a fadin kasar nan.