Jihohi sun fara farfaɗo da cibiyoyin kula da lafiya matakin farko guda 17,000

Spread the love

Ma’aikatan kiwon lafiya a matakin farko sun samu karbuwa yayin da gwamnatin tarayya da na jihohi suka kaddamar da farfado da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko (PHCs) guda 17,000 a fadin kasar nan.

Ministan lafiya da walwalar jama’a, Farfesa Ali Pate, ya bayyana haka a lokacin taron ministoci na bikin cika shekara guda da shugaban kasa Bola Tinubu yayi akan karagar mulki cewa an samu Naira biliyan 260 a matakin jiha domin farfado da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko a fadin kasar nan.

Pate ya ce gwamnati ta yi shirin farfado da PHCs guda 8,300 a fadin kasar nan domin samar da cikakken aiki da kuma fadadawa da inganta PHC 17,000 cikin shekaru uku masu zuwa.

Ya bayyana cewa, za a sake farfado da PHCs ne ta hanyar tallafin kudi na IDA da kuma asusun samar da kiwon lafiya na asali BHCPF, ya kara da cewa gwamnatin tarayya na samar da ka’idoji da za su taimaka wa jihohi wajen aiwatar da ayyukan farfado da ayyukan raya kasa don tabbatar da an yi amfani da albarkatun. a hankali don manufar da aka yi niyya.

Wani bincike da jaridar LEADERSHIP ta gudanar a ranar lahadin da ta gabata ya nuna cewa an fara gudanar da aikin a wasu jihohin tarayyar kasar nan yayin da wasu kuma ba a fara tashi ba.

A jihar Gombe, kwamishinan lafiya na jihar, Dakta Habu Dahiru, ya bayyana cewa an fara farfado da hukumar PHC a jihar.


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button